Gwamna ya hada baki da dan kwangila wajen handame N1.8bn - Kakakin majalisar Kwara
Kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Yakubu Danladi, ya zargi tsohon gwamnan jihar, AbdulFatah Ahmed, da almundahanan kudi N1.8bn na gyara hanyar da ba'ayi ba.
Kakakin ya ce tsohon gwamnan ya biya dan kwangila kudin da sunan gyaran hanya mai tsawon kilomita 33 na Ilesha zuwa Gwanara a karamar hukumar Kaiama da karamar hukumar Baruten na jihar.
Danladi ya bayyana haka ne yayinda yake magana da manema labarai yayin bikin murnar cika shekara daya da sabuwar majalisa.
Yace: "Tsohuwar gwamnatin jihar nan ta bada kwangilan kwaraskwariman hanyar Ilesha zuwa Gwanara mai kilomita 33 amma babu abinda akayi a wajen."
"Hanyace mai tsawon kilomita 33 da tsohon gwamna, Alhaji AbdulFatah Ahmed, yayi amfani wajen wawura dukiyar jihar Kwara saboda N1.8bn aka biya dan kwangila da sunan ya yi aikin."

Asali: UGC
KU KARANTA WANNAN: Mun yiwa tubabbun ya Boko Haram 900 rijistan katin zama yan kasa - NIMC
Danladi, ya kara da cewa mutan garin basu taba ganin kwalta ba a hanyoyinsu amma gwamna mai ci yanzu, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bada kwangilan zuba kwalta kuma za'a kammala zuwa karshen shekarar nan.
Amma mai magana da yawun tsohon gwamnan, AbdulWahab Oba, ya ce kudin da aka biya dan kwangilan kudin aikin da aka sa shi ne kuma yayi.
Yace: "Mun biya kudin ne bisa irin aikin da ma'aikatar aiki jihar ta bada. Abinda kakakin yake fadi kawai yanayi ne don basar da mutanensa. Mun yi abinda ya kamata lokacin da muke gwamnati."
"Saboda haka gwamnatin da ke ci yanzu ta mayar da hankali wajen yin abin da ya kamata wajen yiwa mutane aiki."
A wani labarin ba zata da ya shigo mana, Sanata mai wakilar mazabar Legas ta gabas, Bayo Osinowa, ya mutu. Dan majalisan ya mutu ne yana mai shekara 65 a asibiti.
Rahotanni sun bayyana cewa Sanatanya mutu ne sakamakon cutar Coronavirus.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng