Mun yiwa tubabbun yan Boko Haram 900 rijistan katin zama yan kasa - NIMC

Mun yiwa tubabbun yan Boko Haram 900 rijistan katin zama yan kasa - NIMC

- Tubabbun yan Boko Haram zasu samu katin zama dan kasa

- Za'a saki tsaffin yan ta'addan 603 a watan Yuli bayan watanni ana lura da su

- Yan Najeriya da dama sun nuna damuwarsu kan shirin sakin tubabbun yan ta'addan

Hukumar rijistan yan kasa NIMC ta ce ta yiwa tubabbun yan ta’addan Boko Haram 900 rijistan katin zama yan kasa.

A takardar da hukumar NIMC ta saki ranar Litinin, ta ce a matsayinta na mai ruwa da tsaki wajen lamarin tsaro a Najeriya, za ta yiwa tubabbun yan Boko Haram katin zama dan kasa kafin mayar da su cikin al’umma.

Shugaban hukumar, Aliyu Aziz, ya jaddada niyyar hukumar wajen baiwa jami’an tsaro abubuwan da suke bukata na labarin yan Najeriya ko da yaushe.

Yace: “Hukumar na da karfin taimakawa gwamnatin tarayya wajen yakar rashin tsaro ta hanyar amfani da kayayyakin aikinta na zamani.”

Mun yiwa tubabbun ya Boko Haram 600 rijistan katin zama yan kasa - NIMC
Tubabbun ya Boko Haram
Asali: UGC

KU KARANTA: Sarakunan gargajiya a Katsina na da hannu cikin hare-haren da ake kaiwa al'ummarsu - Fadar shugaban kasa

Jagoran sashen watsa labaran hedkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya ce hukumar NIMC na daya daga cikin hukumomin da ke taimakawa cikin shirin sauya tunani da canza tsaffin yan Boko Haram.

Enenche ya ce babu dan Boko Haram din da zai yi wuyan kamuwa dan yayi kokarin komawa aikin ta’addanci musamman yanzu da NIMC ta dau labarinsu.

Yace: “Hukumar rijista da sanin yan kasa na daya daga cikin hukumomin da ke taimakawa wajen tattara labaran tubabbun yan Boko Haram saboda hakan zai taimaka wajen bibiyarsu idan wani abu ya faru.”

Enenche ya ce a watan Yuli, za’a saki tubabbun yan Boko Haram 603 bayan an kammala shirin canza musu tunani.

A wani labarin ba zata da ya shigo mana, Sanata mai wakilar mazabar Legas ta gabas, Bayo Osinowa, ya mutu.

Dan majalisan ya mutu ne yana mai shekara 65 a asibiti.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel