Coronavirus: Likitoci, iyaye da malamai sun gargadi gwamnati a kan kada ta bude makarantu yanzu

Coronavirus: Likitoci, iyaye da malamai sun gargadi gwamnati a kan kada ta bude makarantu yanzu

Yayin da ake ci gaba da hurowa gwamnatin tarayya wutar bude makarantu, masu ruwa da tsaki a sashen ilimi da kiwon lafiya sun gargadi gwamnatin a kan kada ta yi gaggawar aiwatar da hakan.

Bayan ci gaba da sassauta dokar kulle da gwamnati ke yi, masu ruwa da tsaki a sashen ilimi da kiwon lafiya sun fayyace alkibilar da suka fuskanta dangane da bude makarantu.

Masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi da kiwon lafiya, sun gargadi gwamnatin tarayya da ta jihohi a kan ka da su yi gaggawar bude makarantu a yanzu.

Tun a watan Mayun da ya gabata ne kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona, ya ba da shawarar a iya bude makarantu bayan da gwamnati ta ba da umarnin sassauta dokar kulle.

Sai dai ya zuwa yanzu, gwamnatin ba ta kayyade ranar da za a bude makarantun ba domin dalibai su koma aji wajen daukan darasi.

Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Da ta ke gargadin gwamnatin dangane da yunkurinta kan lamarin komawar dalibai makarantu, kungiyar Likitocin Najeriya NMA, ta ja kunnen gwamnatin da ta yi taka tsan-tsan.

Kungiyar NMA ta ja hankalin gwamnatin a kan kada ta kuskura ta bude makarantu a yanzu domin hakan zai iya mayar musu da hannun agogo baya a fafutikar da ake na dakile yaduwar cutar korona a kasar.

Shugaban kungiyar NMA, Farfesa Innocenta Ujah, ya ce har ila yau akwai sauran rina a kaba dangane da lamarin yaki da cutar korona a kasar nan.

KARANTA KUMA: An kashe Likita, an ƙone gawarsa ƙurmus a jihar Zamfara

Haka kuma kungiyoyin malamai da iyayen dalibai na Najeriya, NAPTAN da NUT, sun gargadi gwamnatin da ta yi dogon nazari da daukan matakai gabanin yanke shawarar bude makarantu.

Kungiyoyin biyu sun ankarar da gwamnatin a kan ka da ta yanke wani hukunci a yanzu wanda daga bisani za ta yi da na sanin zartar da shi a lokaci na gaba.

Babban sakataren kungiyar ma'aikatan binciken lafiya na Najeriya, Dr. Casmir Ifeanyi, ya bayyana damuwa kan yadda mutane ba sa kiyaye matakan kare kai daga kamuwa da cutar korona.

Yayin hararo ingancin matakan kare kai daga kamuwa da cutar korona, Dakta Ifeanyi ya ce lokaci mafi dacewa da ya kamata gwamnati ta ba da umarnin bude makarantu shi ne watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel