Matsalar tsaro ta fi ta annobar korona tashin hankali a Kaduna - Annger ya gargadi El-Rufa'i

Matsalar tsaro ta fi ta annobar korona tashin hankali a Kaduna - Annger ya gargadi El-Rufa'i

Wani babban malamin addini, Rabaran Chris Annger, ya shawarci gwamnatin jihar Kaduna a kan cewa, ta tashi ta farga kan sha'anin tsaro tamkar yadda ta ke yakar annobar korona.

Annger wanda ya kasance mataimakin shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista reshen jihar Kaduna, ya yi gargadin cewa, matsalar tsaro ta fi ta annobar korona tashin hankali a jihar.

Gargadin Rabaran Annger ya zo ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni, kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Ya nemi gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagoranci gwamna Nasir El-Rufa'i, da ta kamanta irin himmar da ta ke yi a yaki da annobar korona wajen kawo karshen kashe-kashe a jihar.

Gwamnan jihar Kaduna; Mallam Nasir El-Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna; Mallam Nasir El-Rufa'i
Asali: Instagram

Babban Limamin na Universal Reformed Christian Church, ya ce kashe-kashen da ake faman yi a jihar wanda a yanzu ya haddasa asarar rayuka da dukiya marar misali abin damuwa ne.

Har ila yau, Annger ya ce akwai bukatar gwamnati ta mike tsaye kan lamarin kashe-kashe wajen shimfida tsauraran matakai tamkar yadda ta ke fafutikar dakile yaduwar cutar korona a jihar.

Da ya ke jawabi yayin gabatar da hudubarsa ta farko bayan sassauta dokar kulle, Annger ya kirayi gwamnati da ta kara himma wajen tabbatar da dawo da zaman lafiya a Kudancin jihar Kaduna.

KARANTA KUMA: PDP ta zargi APC da yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi

Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamna El-Rufai ya ce bayan sassauta dokar kulle da yayi a jihar, mataki na gaba shi ne kiyaye yaduwar annobar korona wacce take hannun mutanen jihar.

El-Rufai ya roki jama'ar jihar da su dauki dawainiyar yaki da yaduwar cutar korona. Ya ce kada a mayar da kokarin da yayi a baya ta hanyar kin kiyaye dokokin hana yaduwar cutar.

Gwamnan wanda ya yi wannan sanarwa a ranar Talata, ya mika sakon godiyarsa ga jama'ar jihar Kaduna a kan yadda suka yi hakurin watanni biyu da rabi wurin dakile annobar.

"Mu mutunta sadaukarwar da muka yi ta hanyar tallafawa kanmu tare da dakile yaduwar muguwar cutar."

Kun yi babban kokari ta yadda kuka zauna a gida na makonni goma. "Mu nuna cewa za mu iya zama lafiya duk da sassauta dokar da aka yi," ya kara da cewa.

El-Rufai ya yi kira ga dattawan da suka wuce shekaru 50 da su zauna a gida duk da sassauta dokar hana walwalar da aka yi a jihar Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel