Abinda yasa Aisha Buhari ta ki yin tsokaci a kan cece-kucen jama'a - Hadiminta

Abinda yasa Aisha Buhari ta ki yin tsokaci a kan cece-kucen jama'a - Hadiminta

Aliyu Abdullahi, kakakin uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce uwar dakinsa ta daina magana a kan al'amarin da ya faru tsakaninta da Sabiu Yusuf saboda sun juya manufarta.

Abdullahi, wanda ya zanta da gidan talabijin din Channels a ranar Lahadi, ya ce har a halin yanzu hadimanta da aka garkame suna tsare ba a sako su ba.

Uwargidan shugaban kasar cikin kwanakin nan ta yi wa sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, kiran gaggawa a kan sakin hadimanta da ya tsare.

A yayin da aka tambayi hadimin uwargidan shugaban kasar ko suna nan tsare har yanzu, ya ce, "har a halin yanzu suna hannun 'yan sanda. Na san shugaban jami'an tsaron, kwamandan masu mata rakiya da 'yan sandan ofishinta duk suna tsare.

"Tana yin magana a gaban kowa amma ta daina magana ne saboda mutane basu fahimtarta kuma suna juya maganarta.

"Amma gaskiya a koda yaushe tana yin fatan alheri ga kasar nan ta yadda daga ita har 'ya'yanta za su samu natsuwa ko bayan sun sauka mulki."

Sakataren shugaban kasar mai zaman kansa, Yusuf Sabiu wanda ya dawo daga Legas ya ki killace kansa amma sai ya kutsa zuwa fadar shugaban kasa.

An gani cewa hadiman uwargidan shugaban kasar sun fitar da shi daga fadar ta karfi da yaji, lamarin da yasa aka damke dukkan masu tsaron lafiyarta har da shugabansu, Usman Shugaba.

Abinda yasa Aisha Buhari ta ki yin tsokaci a kan cece-kucen jama'a - Hadiminta
Abinda yasa Aisha Buhari ta ki yin tsokaci a kan cece-kucen jama'a - Hadiminta. Hoto daga Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dan siyasa ya yi rabon igiyoyi ga mutanen mazabarsa a Arewa (Hotuna)

Rashin kwanciyar hankali ya cika fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan janye dukkan jami'an tsaron lafiyar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari da aka yi.

Janye jami'an 'yan sandan da ke kula da ofishin uwargidan shugaban kasar ya biyo bayan rikicin da ya shiga tsakanin matar shugaban kasan da dan uwan Buhari, Sabiu Tunde Yusuf.

Rikicin ya fara ne tun bayan da uwargidan shugaban kasar ta bukaci Tunde da ya kiyaye dokokin dakile yaduwar annobar korona na killace kai tsawon kwanki 14 bayan an yi tafiya.

Aisha Buhari ta tsinkayi gidan dan uwan shugaban kasar tare da yaranta inda sa'in'sar su ta kai ga shigar jami'an tsaronta wadanda suka harba bindiga har sau uku a iska.

A ranar Lahadi, jaridar Daily Trust ta gano cewa an samu harbe-harben wanda aka yi wa dan uwan shugaba Buhari mai suna Sabiu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: