Tsaro: Buhari ya yiwa Ango Abdullahi 'wankin babban bargo'

Tsaro: Buhari ya yiwa Ango Abdullahi 'wankin babban bargo'

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kwatanta dattijan arewa karkashin shugabancin Ango Abdullahi da masu sukar mulkinsa kawai.

A yayin martani game da kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kungiyar tayi sakamakon karuwar rashin tsaro a arewa, Adesina ya kwatanta kungiyar da rundunar mutum daya wacce akalarta ta zama ra'ayin siyasa tare da tsanar da tayi wa shugaban kasa.

Abdullahi ya ce miyagun hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa na nuna gazawar mulkin Buhari ne wurin samar da tsaro tare da walwalar 'yan kasa.

Amma a martanin da Adesina yayi, ya ce fadar shugaban kasar bata kallon wannan kungiya da kowa face Abdullahi.

"Ba abun mamaki bane kalaman da suka fito daga Farfesa Abdullahi kuma matsayarmu a kan abinda kungiyarsa ta ginu a kai bata sauya ba," yace.

Tsohon shugaban jami'ar ya sa hannu a kan takardar da ya fitar karkashin kungiyar dattawan arewa (NEF), jaridar The Cable ta ruwaito.

Idan aka ji sunan, sai a yi zaton da gaske dattawan ne amma gaskiyar al'amarin shine Ango Abdullahi ne kuma Ango Abdullahi ne kungiyar dattawan arewan.

"Kungiya ce bahaguwa da bata da wani mamba abun dogaro kuma shugabannin suna yaki ne ba tare da runduna ba," Adesina yace.

Kakakin shugaban kasar ya ce rundunar mutum dayan mai suna NEF ta nuna halinta karara ga Buhari tun kafin zaben 2019 amma sai aka daga dan takararta aka mishi mugun kaye.

Tsaro: Buhari ya yi Ango Abdullahi 'wankin babban bargo'
Tsaro: Buhari ya yi Ango Abdullahi 'wankin babban bargo'
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Janye hadiman Aisha Buhari ya kawo rikici a fadar shugaban kasa

Idan za mu tuna, kungiyar dattijan arewa (NEF) ta koka a kan halin rashin tsaro da arewa ke ciki tare da zargin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da gaza yin maganin matsalar.

A cikin wani jawabi da ya fito ranar Lahadi, jagoran kungiyar, Ango Abdullahi, ya ce lamari rashin tsaro ya na kara tabarbarewa a kullum.

Ya ce yawaitar hare - haren 'yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram ke kaiwa alama ce da ke nuna cewa gwamnatin Buhari "ta fadi kasa warwas" a bangaren tsaro da walwalar 'yan kasa.

"Kungiyar dattijan arewa ta damu matuka a kan yawaitar hare - hare da asarar dukiya a yankin arewacin Najeriya.

"Yadda 'yan bindiga suke cin karensu babu babbaka ya nuna cewa yanzu yankin arewacin Najeriya yana hannun 'yan ta'adda, sai yadda suka ga dama suke yi.

"A bayyane take cewa gwamnatin Buhari da gwamnatocin jihohi sun rasa yadda zasu bullowa lamarin, sun gaza kare rantsuwar da suka yi a kan cewa zasu kare jama'a da dukiyoyinsu.

"Lamarin tsaro kullum kara tabarbarewa yake yi saboda 'yan ta'adda sun fahimci cewa akwai raunin shugabanci a wannan gwamnati, lamarin da ya basu karfin gwuiwar kai munanan hare - hare a kan jama'a," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel