Yanzu-yanzu: Mutum 403 sun sake kamuwa da korona, jimilla ta kai 16,085

Yanzu-yanzu: Mutum 403 sun sake kamuwa da korona, jimilla ta kai 16,085

Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cutattuka masu yaduwa (NCDC) ta bayyana a yau Lahadi, 14 ga watan Yunin 2020, mutum 403 sun sake harbuwa da cutar korona a Najeriya.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, jihar Gombe ta samu karin mutum 73 masu muguwar cutar yayin da jihar Legas ta samu karin mutum 68 da ke dauke da cutar.

Babban birnin kasuwancin Arewa, jihar Kano ta samu karin mutum 46 masu muguwar cutar yayin da jihar Edo ke da karin mutum 36.

Babban birnin tarayyar kasar nan, Abuja, ya samu karin mutum 35 yayin da makwabciyarta jihar Nasarawa ke da karin mutum 31.

Jihar Kaduna da ke yankin arewa ta samu karin mutum 17 yayin da jihar Oyo ta samu karin mutum 16.

Jihar Abia da ke kudancin Najeriya ta samu karin masu cutar har 15 yayin da jihohin Delta da Borno ke da karin goma sha uku-uku.

Jihar Filato na da karin mutum 8 yayin da jihohin Niger da Ribas ke da karin mutum bakwai-bakwai.

Jihohin Enugu da Ogun na da karin mutum shida-shida da suka harbu da cutar yayin da Kebbi ke da karin mutum 3.

Jihohin Ondo, Anambra da Imo na da karin mutum daddaya da suka harbu da cutar.

Jimillar masu cutar a fadin Najeriya ta kai 16,085 yayin da aka sallama mutum 5,220 daga asibiti bayan warkewa tas daga cutar.

Mutum 420 ne suka rasu sakamakon muguwar annobar da ta game duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel