'Yan bindiga sun halaka mutum 10 a harin sassafe

'Yan bindiga sun halaka mutum 10 a harin sassafe

- Wani sabon harin yan bindiga ya yi sanadiyar rasa rayuka akalla guda goma a jihar Binuwai

- Usman Suleiman, shugaban karamar hukumar Agatu ya tabbatar da harin wanda ya afku a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni

- A bisa ga rahoton, harin ya afku ne a garuruwa uku da ke karamar hukumar Agatu

A kalla mutum 10 suka rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a karamar hukumar Agatu da ke jihar Binuwai.

Daily Trust ta gano cewa a halin yanzu an samu gawawwaki 10 amma kuma wasu sun bace sakamakon harin.

Shugaban karamar hukumar Agatu, Usman Suleiman, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Daily Trust ta waya, ya ce har yanzu babu wani cikakken bayani game da harin sassafen.

'Yan bindiga sun halaka mutum 10 a harin sassafe
'Yan bindiga sun halaka mutum 10 a harin sassafe Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Suleiman ya ce wurin karfe 7:00 na safe aka sanar da shi cewa mahara sun kai hari yankin kuma an gaggauta sanar da mataimaki na musamman a kan tsaro tare da rundunar Operation Whirl Stroke.

Ya jaddada cewa jami'an tsaron sun gaggauta kai dauki inda suka kama wasu matasa kuma sun samu gawawwaki tara.

Wani mazaunin yankin ya ce an samu bindiga kirar AK47 da harsasai 60 daga hannun shugaban 'yan bindigar wanda ya shiga hannun rundunar Operation Whirl Stroke.

Har ila yau, kwamandan rundunar OPWS, Manjo janar Adeyemi Yekini ya ki yin tsokaci a kan al'amarin amma ya bukaci manema labarai da su tuntubi sashen yada labarai na hedkwatar tsaro.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Binuwai, DSP Catherine Anene, ya tabbatar da cewa an samu gawawwaki uku sakamakon harin.

KU KARANTA KUMA: Edo 2020: APC ta bukaci korar Obaseki da wasu mutum biyu

Anene ya ce, "Bayanan da muka samu a ranar Lahadi da misalin karfe 5:30 na safe ya nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyen Adama, yankin ruwa na Agatu inda ababen hawa basu zuwa.

"Tuni aka tura jami'an tsaro yankin amma har yanzu ba a tabbatar da yawan barnar da aka yi ba. Za a sanar muku da duk ci gaban da aka samu, in ji shi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel