Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan harbe - harbe a Villa
Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan harbe-harben bindigar da wani jami'in tsaro da ke gadin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ya yi a Villa.
A ranar Juma'a ne rahotanni suka bayyana cewa wasu jami'an tsaro, a karkashin umarnin Aisha Buhari, sun tunkari Sabiu Yusuf, hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Rundunar 'yan sanda ta kama wasu hadiman Aisha Buhari sakamakon harbe - harben da aka yi a fadar shugaban kasa.
Sai dai, Aisha Buhari ta bukaci babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya saki jami'an tsaron da ke bata kariya.
Da farko dai fadar shugaban kasa ta yi gum a kan faruwar lamarin tare da kin bayyana takamaiman halin da ake ciki dangane da batun.
Amma, a cikin wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi, ya ce shugaba Buhari ya bayar da umarni a gudanar da bincike a kan lamarin.
"Fadar shugaban kasa ta yaba da yadda jama'a suka nuna damuwarsu a kan hatsaniyar da ta kai ga 'yan sanda sun kama wasu mazauna fadar shugaban kasa.
"Mu na bawa jama'a tabbacin cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba ya fuskantar wata barazana daga cututtuka ko kuma daga jami'in tsaron da ake gudanar da bicike a kansa.
DUBA WANNAN: Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin Dogo Gide, sansanin 'yan bindiga mafi girma
"Lamarin ya faru ne a wajen gidan da shugaba kasa ya ke zaune. Ma su tsaron lafiyar shugaban kasa kwararru ne da aka bawa horo a kan sarrafa makamai da kuma bayar da kariya a yayin da basa dauke da makamai.
"Shugaban kasa ya yi aiki da tsarin doka ta hanyar bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike a kan faruwar lamarin.
"Bai kamata saboda samun karamin sabani 'yan adawa suke kafa hujja a kan cewa an kaiwa shugaban kasa hari ba.
"A wannan karo, kamar koda yaushe, shugaban kasa ya ce a bari doka ta yi aikinta," a cewar Garba Shehu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng