Tattalin arziki: Sanusi II ya yi muhimmin kira ga gwamnatin tarayya, ya yi gagarumin hasashe

Tattalin arziki: Sanusi II ya yi muhimmin kira ga gwamnatin tarayya, ya yi gagarumin hasashe

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya tana shirin fadawa bashin da ba za ta iya biya ba idan ta ci gaba da tafiya da irin salon shugabancinta.

Kamar yadda The Punch ta bayyana, Sanusi ya sanar da hakan ne a wani shiri da Emmanuel Chapel ya jagoranta mai taken 'hanyar shafe illar COVID-19 ga tattalin arziki da kuma hanyar farfadowa'.

Ba tun yanzu ba Sanusi yake kira ga gwamnatin tarayya da ta rage yawan kudin da take kashewa don hakan ba zai kawo daidaituwar tattalin arziki ba.

Ya ce kamata yayi gwamnati ta kara yawan hanyoyin samar da kudi ta hanyar kara ma'aikata a fannonin kiwon lafiya da ilimi.

"Ina da tabbacin cewa raguwar kudin shiga a bangarorin man fetur zai sa kila sai mun ci bashi don biyan ma'aikata albashinsu. Dole ne mu sake duba tsarin," yace.

"A cikin kundun tsarin mulki, dole ne mu samu shugaban kasa da mataimakinsa. Dole ne mu samu minista daga kowacce jiha ta kasar nan, sanatoci 109 da kuma mambobin majalisar wakilai 360.

"Hakazalika, dole ne mu samu gwamnoni 36, mataimakansu 36 da kuma 'yan majalisa a kowacce jiha.

"Dole ne a samu shugabannin kananan hukumomi 774 a fadin kasar nan kuma tilas ne su samu masu bada shawara da kuma mataimaka daban-daban.

Tattalin arziki: Sanusi II ya yi muhimmin kira ga gwamnatin tarayya, ya yi gagarumin hasashe
Tattalin arziki: Sanusi II ya yi muhimmin kira ga gwamnatin tarayya, ya yi gagarumin hasashe. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutum 403 sun sake kamuwa da korona, jimilla ta kai 16,085

"Daga wannan kiyasin, mun shirya cin bashin da ba za mu iya biya ba. Ina ta maganar nan na tsawon shekaru.

"A wannan tsarin da muke bi, za mu samu daidaito kuwa zuwa wani lokaci? Wannan tattaunawar ce ya kamata mu dinga yi a kasar nan." Yace.

A wani labari na daban, Dele Momodu, fitaccen dan jarida da ya taba yin takarar shugaban kasa, ya ce ya zabi ya goyi bayan Atiku a zaben 2019 saboda babu abinda ya ke sauyawa a tattare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A cewar Momodu, gwamnatin shugaba Buhari ta gurgunta 'yancin cin gashin kai na majalisun kasa da bangaren shari'a.

Yayin wata hira da shi a wani shiri mai taken 'Osasu Show', Momodu ya ce jam'iyyar APC ta yaudari masu zabe, ta yaudari sojoji, sannan ba mulkin dimokradiyya ta gaskiya suke yi ba.

"Maganar gaskiya jam'iyyar APC ba ta nuna cewa za ta iya sauya komai ba kamar yadda ta dauki alkawari a shekarar 2015.

"Na yi rubutu daban - daban zuwa shugaban kasa amma duk da haka babu abinda ya sauya, ya zama dole na kara gaba domin na gwada wani mutumin," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel