Kasashe masu yawa suna rokon abinci daga Najeriya yayin kulle - FG

Kasashe masu yawa suna rokon abinci daga Najeriya yayin kulle - FG

Gwamnatin tarayya ta ce kasashen da ke da makwabtaka da Najeriya suna rokarta abinci a yayin kulle don rage radadin annobar Coronavirus.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin hirar Instagram ta kai tsaye da City People Magazine.

Ministan, wanda ya yi magana a kan shirye-shiryen daidaituwar tattalin arziki wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya mika ga Manjo janar Muhammadu Buhari, ya ce anyi wannan shirin ne don fadada hanyoyin habakar tattalin arziki don rage radadin annobar Coronavirus.

Fashola ya ce, "Muna tunanin samar da tituna da duwatsu, siminti, rodi da sauransu. Ta hakan za mu dauka mutane da yawa aiki. Mutum 14 za su iya gama kilomita daya.

"Noma da kiwo ya fi tasiri a bangaren daidaituwar tattalin arziki. Muna fatan habaka fannin noma da kiwo a fadin kasar nan. A halin yanzu kashi daya bisa uku na gonakinmu muke nomawa.

"Muna bukatar fadada bangaren tare da kara yawan noman da ake yi a kasar nan.

"Zan iya cewa mun samu nasarori a harkar noma don a a yayin da annobar korona ta barke, muna ta samun wasiku daga kasashen kusa da nesa masu bukatar abinci.

"Buhari ya bukaci a ciyar da jama'ar kasar nan kafin a bai wa wasu abinci. Bamu san yaushe wannan al'amarin zai zo karshen ba."

Kasashe masu yawa suna rokon abinci daga Najeriya yayin kulle - FG
Kasashe masu yawa suna rokon abinci daga Najeriya yayin kulle - FG. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Janye hadiman Aisha Buhari ya kawo rikici a fadar shugaban kasa

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci masu manyan masana'antun jihar da su gaggauta miko tsare-tsaren sake budesu a jihar.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya fitar a ranar Litinin, jaridar The Punch ta ruwaito.

Takardar ta ce, Ganduje ya bada wannan umarnin a yayin taro na musamman da ya yi da manyan masu masana'antu na jihar.

Ya ce an yi taron ne don shirya yadda za a dakile kalubalen da ake shirin fuskanta sakamakon annobar korona.

"A halin yanzu, muna bukatar sabbin tsare-tsare da za mu yi amfani da su wurin bude masana'antun ba tare da wani hatsari ga rayukan ma'aikata ba.

"Ina da tabbacin za a fitar da sabbin tsare-tsaren nan ba da dadewa ba don ganin hanya mafi sauki da za mu fuskanci kalubalen da ke gabanmu," Ganduje yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel