An samu karin masu korona 501 a Najeriya, jimilla 15,682
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 501 a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.42 na daren ranar Asabar 13 ga Yuni na shekarar 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 501 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;
Lagos-195
FCT-50
Kano-42
Kaduna-27
Edo-26
Oyo-22
Imo-21
Gombe-17
Benue-12
DUBA WANNAN: Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake kashe wani basarake a Katsina
Enugu-12
Delta-11
Anambra-11
Ebonyi-10
Nasarawa-9
Ogun-9
Bauchi-8
Kebbi-4
Akwa Ibom-3
Jigawa-3
Katsina-3
Yobe-2
Borno-2
Kwara-1
Ondo-1
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Asabar 13 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 15682.
An sallami mutum 5101 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 407.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji mazauna garin Zaria a ranar Juma'a sunyi murnar bude masallatan Juma'a a birnin Zazzau da wasu garurruwa da ke jihar ta Kaduna.
Tun misalin karfe 8 na safe ne mutane da dama suka yi wanka suka saka kayatattun kayansu domin shirin zuwa salla a masallatan Juma'a da suke raayin zuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kazalika wasu daga cikin masallatan suna kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka bayar da shawawarin a rika kiyaye wa domin dakile yaduwar cutar coronavirus.
Wani mazaunin Zaria, Malam Ibrahim Danllami ya ce mafi yawancin yara a birnin ta Zazzau sun dauki Juma'ar ta jiya tamkar ranar Sallar Idi ne a wurinsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng