'Da yardarsu muke saduwa', inji magidancin da ke zina da 'ya'yansa mata biyu
Wani magidanci mai yaya shida, Peter Ayemoba da aka kama saboda yana saduwa da 'ya'yansa mata biyu ya ce ya fara saduwa da su ne tun bayan rasuwa matarsa wato mahaifiyarsu.
Ya kuma ce da amincewar 'ya'yansa ne ya ke saduwa da su ba tilasta su ya yi ba.
Yan sandan jihar Niger ne suka kama Ayemoba a wannan makon bayan yayansa biyu masu shakara 22 da 20 sun yi kararsa zuwa wani dan uwansu da ya kira 'yan sandan.
Da yan sanda suke masa tambayoyi, Ayemoba ya shaidawa yan sanda cewa ya fara saduwa da 'ya'yansa biyun ne tun bayan da matarsa wato mahaifiyar yayan ta rasu shekara bakwai da suka shude.
"Na fara saduwa da 'ya'ya na kimanin shekara bakwai da suka gabata bayan rasuwar mata ta a 2013. Rasuwarta ya gigita ni ban san lokacin da na fara saduwa da 'ya'ya na ba.
"Rasuwar mata ta ya rikita ni har ta kai ga ban san abinda na ke yi ba. Ina zargin wani ne ya min asiri saboda abinda na rika aikatawa shekara bakwai da suka wuce ba aikin hankali bane.
"Bayan rasuwar mata ta na shaku da yaya na har ta kai ga na fara saduwa da su. Ba zan iya fadin dalilin da yasa na yi wa 'ya'ya na haka ba. Kawai dai zuciya ta tana raya min cewa ba ni ne mahaifi na farko da ya fara saduwa da 'ya'yan sa ba," inji Ayemoba.
DUBA WANNAN: Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake kashe wani basarake a Katsina
Ya cigaba da cewa, "Bayan rasuwar mata ta ne naji na fara shaawar yaya na. Na kan je dakinsu muyi wasa daga nan kuma muka fara saduwa amma da amincewarsu.
"Duk lokacin da suka nuna ba su so, na kan fada musu cewa ina kokarin ganin mun shaku ne tunda mahaifiyarsu ta mutu.
"Wasu lokutan na kan yi barazanar zan kashe kai na idan ba su bari na sadu da su ba. Wata rana nayi musu misali da Lot a Bible da ya sadu da 'ya'yansa kuma Allah bai hukunta shi ba. Na fada musu ba laifi bane shiyasa aka rubuta a Bible."
Ayemoba ya ce matarsa ta biyu da 'ya'yansa maza hudu ba su san abinda ke faruwa tsakaninsa da yayansa mata ba.
"Yaya na mata sun matsa min na sake aure amma duk da haka na kan sadu da su a duk lokacin da na samu dama. Akwai buktar in tafi in nemi taimako don abinda na aikata ba lafiya bane," in ji shi.
A cewarsa, da yardar 'ya'yansa mata ya ke saduwa da su.
"Da amincewarsu muke aikata abinda muke yi. Abinda ke bani mamaki shine tsawon shekarun da muka yi muna saduwa cikin farin ciki. Kwatsam kawai sai suka yi kara ta wurin dan uwan mu shi kuma ya gayyato 'yan sanda.
"Nayi mamakin abinda suka yi, wata kila dai tura ta kai bango ne saboda haka a zartar min da hukuncin da doka ta tanada."
Yan sanda sun ce za a gurfanar da shi a kotu nan ba da dadewa ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng