Boko Haram sun kashe mutum 81 bayan sun nuna wa soji maboyarsu - DHQ

Boko Haram sun kashe mutum 81 bayan sun nuna wa soji maboyarsu - DHQ

Hedkwatar tsaro ta ce mayakan ta'addancin Boko Haram sun kashe mutum 81 a jihar Borno saboda 'yan garin sun nuna wa sojoji maboyar 'yan ta'addan.

A yayin zantawa da gidan talabijin na Channels a yammacin Juma'a, John Eneche, mai magana da yawun rundunar sojin, ya bayyana rashin sirri a matsayin babban kalubalen da ke kawo koma baya a yaki da tsaro a yankin Arewa.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, mayakan ta'addancin Boko sun kai hari kauyen Faduma Kolomdi da ke karamar hukumar hukumar Gubio ta jihar Borno inda suka kashe jama'a da dama.

Daya daga cikin wadanda suka tsallake harin ya ce: "Sun tattara mu tare da cewa za su yi mana wa'azi. Sun bukaci mu mika dukkan makamanmu amma ba kakkautawa sai suka fara harbe-harbe. Hatta yara da mata basu sassauta musu ba."

Yayin shirin gidan talabijin, Enenche ya ce wannan harin tare da na jihar Katsina duk sun faru ne saboda mazauna yankin sun sanar da jami'an tsaro maboyar 'yan bindigar.

Boko Haram sun kashe mutum 81 bayan sun nuna wa soji maboyarsu - DHQ
Boko Haram sun kashe mutum 81 bayan sun nuna wa soji maboyarsu - DHQ. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Rikici tsakanin dan uwan Buhari da Aisha Buhari: An ji harbin bindiga a Aso Rock

Ya ce: "Mutane da yawa basu san abinda muka gani a kwanakin da suka gabata ba. A Borno da Katsina an kashe mutum 81 da kuma 40. Dalilin kawai shine mazauna yankin sun sanar da jami'an tsaro maboyar 'yan ta'addan.

"Da za mu samu hadin kai daga jama'ar yankin da 'yan ta'addan suke, da tuni mun gama halaka 'yan ta'addan.

"A lokacin da suka fara bamu bayanai, muna samun nasarori masu tarin yawa. Daga harin sama har na kasa duk suna yuwuwa ne bayan an samu bayanan sirri daga jama'a."

Enenche ya ce rundunar sojin Najeriya na kokarin karantar ayyukan sauran dakarun duniya kuma ta gano bayanan sirri na da matukar amfani ga nasarorinsu.

"Da kaina na karanci kasar Pakistan. Sun kwashe shekaru 25, bayan shekaru 12 ne jama'a suka fara bada bayanan sirri. Cikin shekaru biyu kacal suka kammala komai. Sannan suka samu zaman lafiya," kakakin rundunar tsaron ya sanar.

Ya kara da cewa, "Zan iya cewa da akwai bayanai, da tuni mun wuce nan. Ka duba, mutum na wucewa daga wuri sai a dasa abu mai fashewa kuma mutane na kallo.

"Wa zaka dora wa laifi? Kansu ko rashin kayan aiki? Babban kalubalenmu shine rashin bayanai."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
NDA
Online view pixel