Allah ya yi wa mataimakin shugaban fadar Gwamna Oyetola rasuwa

Allah ya yi wa mataimakin shugaban fadar Gwamna Oyetola rasuwa

Adejare Adebisi, mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya rasu.

A cewar Ismail Omipidan, babban sakataren watsa labarai na gwamnan da ya fitar da sanarwar ta shafin Twitter na gwamnatin jihar, Adesibi ya rasu ne a daren ranar Juma'a bayan gajeruwar rashin lafiya.

Gwamnatin jihar ta ce mutuwar Adebisi ba ta da alaka da annobar COVID-19.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 54 a duniya.

DUBA WANNAN: Yan ɗamfarar da aka kama da katin ATM 36 sun bayyana yadda suke yaudarar mutane

Omipidan ya ce, "Ya rasu a daren jiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, mutuwarsa ba ta da alaka da annobar COVID-19.

"Za ayi jana'izar Adebisi a dafiyar yau a garin Illobu a jihar Osun."

Gwamnan ya mika sakon ta'aziya ga iyalan mamacin inda ya ce mutuwar Adebisi babban rashi na a gare shi.

Ya ce, "Labarin rasuwarsa mataimakin shugaban ma'aikatan fada na, Jare Adebisi ya kada ni."

"Rasuwarsa babban rashi ne gare ni da mutanen Illobu da jihar baki daya.

"Amma a matsayin mu na musulmi, mun rungumi kaddara tare gode wa Allah cewa marigayin ya yi rayuwa ta gari.

"Ina mika ta'aziya ta ga daukakin iyalansa, jamiyyar APC, 'yan siyasa, gwamnati da jihar baki daya. Za muyi kewarsa sosai. Ina adduar Allah ya saka masa da Aljanna Firdausi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel