Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake kashe wani basarake a Katsina

Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake kashe wani basarake a Katsina

Kimanin yan bindiga 50 a ranar Asabar suka kai hari kauyen Mazoji da ke karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina inda suka kashe dagajin kauyen kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Yan bindigan sun kashe Sarkin Fulanin Fafu, Alhaji Dikko Usman ne a daren ranar Jumaa yayin da suka kai hari a gundumar ta Mazoji da ke Katsina.

Wannan na zuwa ne makonni uku bayan wasu yan bindigan sun kashe hakimin Yantumaki a karamar hukumar Danmusa na jihar, Alhaji Maidabino.

Wata majiya ta shaidawa SaharaReporters cewa yan bindigan sun isa kauyen ne misalin karfe 2 na dare inda suka kashe awanni suna cin karensu babu babbaka har suka kashe dagajin kauyen.

Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake kashe wani basarake a Katsina
Da ɗumi-ɗumi: 'Yan bindiga sun sake kashe wani basarake a Katsina. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yan ɗamfarar da aka kama da katin ATM 36 sun bayyana yadda suke yaudarar mutane

An kuma ruwaito cewa yan bindigan sun kone babura biyar yayin harin inda suka kuma sace shanu masu yawa da ba a tabbatar da adadinsu ba a yanzu.

Majiyar ya koka cewa har zuwa karfe 7:30 na safe babu wani jamin tsaro da ya iso kauyen domin kawo musu dauki.

A baya bayan nan dai yan bindiga da masu satar mutane domin karbar kudin fansa suna baje kolinsu a jihar ta Katsina wadda hakan ya jawo zanga zanga daga mazauna jihar.

A wani labari da Legit.ng ta wallafa, Gwamna Masari na jihar Katsina ya ce baya bukatar wani ofishin siyasa idan ya kammala mulkinsa a 2023.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa akwai rahotanni da ke nuna cewa Masari na hangen majalisar dattawa bayan ya kammala wa'adin mulkinsa.

Masu kira ga Masari da ya nemi kujerar Sanata sun dogara ne da gogewarsa tun bayan da yayi kakakin majalisar wakilai da kuma wannan mulkin jihar Katsina da yayi.

Amma kuma, yayin jawabi ga manema labarai a ranar damokaradiyya ta 2020 a Katsina, gwamnan ya ce, baya bukatar amsa kiran kowa don neman kujerar Sanata.

Masari ya yi bayanin cewa zai cika shekaru 73 a yayin da zai kammala wa'adin mulkinsa karo na biyu a matsayin gwamna.

Ya ce, "Bayan cikar wa'adin mulkina, zan zauna a gida in huta tare da bai wa matasa damar bada gudumawa a siyasa.

"Ban taba tsammanin zan shiga siyasa ba. Na fara aikin gwamnati amma daga baya aka nada ni kwamishina har sau biyu.

"Daga baya jama'a suka bukaci da in wakilcesu a majalisar wakilai wanda na yi nasara a zabe har na yi kakaki.

"Bana tunanin ina bukatar komai a yanzu. Na shiga siyasa ne saboda Allah ya tsara kuma na samu gogewa sosai a rayuwa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel