Ganduje ya bada umurnin bude gidajen kallo, ya basu gudunmuwar takunkumin fuska 40,000

Ganduje ya bada umurnin bude gidajen kallo, ya basu gudunmuwar takunkumin fuska 40,000

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umurnin bude gidajen kallon dake jihar.

Ya bada wannan umurnin ne yayinda ya karbi bakuncin mambobin kungiyar gidajen kallo a jihar Kano ranar Juma'a.

Ya yi kira ga masu gidan kallon su tabbatar da cewa an baiwa juna tazara a gidajen kallonsu.

Gwamnan ya basu gudunmuwar takunkumin rufe baki guda 40,000 saboda suyi amfani da su wajen kalle-kallensu.

Yace: "Yana cikin shawaran da muka yanke na farfado da tattalin arziki ta hanyar bude kasuwanni da cibiyoyin jihar, shi yasa na bada umurnin bude dukkan gidajen kallo fari daga yau,"

Ya yi kira da su suyi amfani da cibiyoyin kallunsu domin wayar da kan matasan jihar domin su taimaka wajen kawo karshen wannan annobar.

Shugaban kungiyar masu gidajen kallo, Sharu Rabi'u Ahlan, ya yabawa gwamnan bisa matakan da ya dauka wajen dakile annobar kuma ya bada tabbacin mambobin kungiyarsa.

KU KARANTA: Sarkin Saudiyya da Yariman Saudiyya sun yi alhinin kisan mutane a Arewacin Najeriya

Ganduje ya bada umurnin bude gidajen kallo, ya basu gudunmuwar takunkumin fuska 40,000
Ganduje
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel