Katsina: Sabon harin 'yan bindiga ya halaka mutum 7, ciki har da mace mai juna biyu

Katsina: Sabon harin 'yan bindiga ya halaka mutum 7, ciki har da mace mai juna biyu

A kalla mutum bakwai suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai kauyukan Kasai da Nahuta da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Jaridar HumAngke ta gano cewa, mutum shida ne ruwa ya ci wanda ya hada da mace mai juna biyu a yayin da suka yi yunkurin tserewa daga kauyen sakamakon harin.

Ganau ba jiyau ba, sun ce 'yan bindigar sun kashe mutum daya a harin yayin da ake neman mutane biyu wadanda ake zargin sun bace duk da 'yan bindigar sun kwashe musu kadarori.

An gano cewa kauyawan sun arce zuwa daji don gujewa harin yayin da 'yan bindigar suka dinga harbin duk abinda suka yi ido biyu da shi.

Mustapha Ruma, wanda ya tsallake harin, ya ce 'yan bindigar sun tsinkayi kauyukansu ne a babura rike da miyagun makamai a yayin da jama'a ke sallar jam'i.

Ya bada labarin yadda maharan suka ci karensu babu babbaka a kauyukan biyu na sa'o'i masu yawa ba tare da tallafi daga jami'an tsaro ba duk da sanar musu da aka yi.

Katsina: Sabon harin 'yan bindiga ya halaka mutum 7, ciki har da mace mai juna biyu
Katsina: Sabon harin 'yan bindiga ya halaka mutum 7, ciki har da mace mai juna biyu. Hoto daga HumAngle
Asali: UGC

KU KARANTA: Rikicin majalisar jihar Kaduna: An yi wa dan majalisa mugun duka (Bidiyo)

Ya ce "gawawwaki shida aka samu a kogin garin a safiyar Asabar a lokacin da muke komawa gari daga dajin da muka boye.

"An yi ruwa mai karfi a ranar kuma daya daga cikinsu mace ce mai juna biyu. Mahaifina ne ya sanar da sarkin ruwa wanda ya aika jama'arsa kogin kafin a samo gawawwakin."

Ya bayyana cewa duk sojojin da aka tura yankin basu kai musu tallafi matukar 'yan bindigar sun bayyana.

A yayin jawabin Ruma a ranar Asabar da dare, ya ce an kai wa wani kauye mai suna Salihawar Dan Alhaji hari a Batsari a daren.

Ya ce kauyen na da nisan kilomita 6 daga Batsari, hakan yasa suke jin harbin bindiga daga yankin.

Yankin arewa maso yamma a halin yanzu ta zama dandalin 'yan ta'addan da 'yan bindigar daji. Suna cin karensu babu babbaka inda suke kashe jama'a, satar Shanu tare da yi wa mata fyade.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel