Sarkin Saudiyya da Yariman Saudiyya sun yi alhinin kisan mutane a Arewacin Najeriya

Sarkin Saudiyya da Yariman Saudiyya sun yi alhinin kisan mutane a Arewacin Najeriya

Hadimin Masallatan Haramaini, Sarkin Salman, da Yarima mai jiran gado, Muhammad Bin Salman, sun aika sakon ta'aziyya ga shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Sun aika ta'aziyyan ne bisa harin yan ta'adda da yayi sanadiyar kisan yan Arewacin Najeriya ranar Talata, kamfanin dillancin labarai Saudi ta ruwaito.

A sakon ta'aziyyar, Sarki Salman ya yi alhinin aikin ta'addancin nan inda ya bayyana cewa Saudiyya na tare da kasar Najeriya da al'ummarta.

Hakazalika Yarima mai jiran gado, Muhammad Bin Salman, ya aika nasa sakon na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari.

A wasikarsa, Yariman ya yi Alla-wadai da wanna hari kuma ya jajantawa shugaban kasa da iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Bugu da kari, ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta yi alhinin wadannan hare-haren.

Sarkin Saudiyya da Yariman Saudiyya sun yi alhinin kisan mutane a Arewacin Najeriya
Sarkin Saudiyya da Yariman Saudiyya Credit: Saudi Agency
Asali: Facebook

KU KARANTA: - Tsohon dan takaran shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce akwai kunya har yanzu sun kasa faranTawa yan Najeriya rai

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Laraba ya tabbatar da kisan mutane 81 da jana'izarsu sakamakon garin da yan ta'addan Boko Haram suka kai Arewacin jihar ranar Talata.

Zulum ya bayyana hakan ne rabar Laraba yayinda yake hira da manema labarai a garin Felo, karamar hukumar Gubio inda harin ya faru.

Bayan kisan mutane 69 a farko, yan ta'addan sun sake komawa suka bankawa gidajen wuta.

Jimamin gwamnan ya bayyana a muryarsa yayinda yake jawabin kan irin kisan gillar da ake yiwa al'ummarsa.

Ya kara tabbatar da rahoton cewa yan ta'addan sun yi awon gaba da mutane shida.

Hakazalika, Akalla mutum 50 ake tunanin cewa sun mutu bayan wani sabon hari da aka kai wani gari na Kadisau da ke cikin karamar hukumar Faskari, jihar Katsina.

Mun samu labari cewa ‘yan bindigan wadanda su ke dauke da manyan makamai sun shiga cikin wannan gari na Kadisau ne da kimanin karfe 4:30 na ranar Talata.

Channels TV ta ce wadannan miyagun mutane sun far ma garin ne a kan babura fiye da 100.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel