Har yanzu bamu yiwa yan Najeriya hallaci ba - Atiku

Har yanzu bamu yiwa yan Najeriya hallaci ba - Atiku

- Tsohon dan takaran shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce akwai kunya har yanzu sun kasa faranTawa yan Najeriya rai

- Atiku ya jinjinawa gwagwarmayan marigayi Moshood Abiola

- Da yiwuwan Atiku ya sake takarar kujerar shugaban kasa a 2023

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce shugabannin siyasan Najeriya har hanzu sun yi kasa a gwiwa wajen farantawa yan Najeriya rai.

A sakon murnar zagayowar ranar demokradiyya, Atiku, ya ce akwai masu baiwa da dama a Najeriya amma rashin shugabancin kwarai ya hana ganosu.

A watan Yunin 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan dokar mayar da 12 ga Yuni, ranar murnar demokradiyya a Najeriya.

Gabanin yanzu, ranar 29 ga Mayu ake murnar demokradiyya.

KU KARANTA: Sau 19 yan Boko Haram suka kai hari Borno cikin watan nan - Kwamandan runduna

Tsohon shugaban kasan ya ce duk da cewan shugabannin Najeriya sun yi iyakan kokarinsu wajen bayar da shugabancin kwarai tun 1999, har yanzu da saura.

Yace: "Murnar ranar Demokradiyya nuna tabbacin irin jajircewanmu ne kan kafa gwamnatin demokradiyya da amincewa da doka."

"Kamar da ya marigayi Bashorun MKO Abiola ke cigaba da zama jarumin gwagwarmayan 12 ga Yuni, akwai ire-irensa irinsu Cif Alfred Rewane; Tafida Shehu Musa Yar’Adua, Alhaja Kudirat Abiola, dss."

"Amma duk da cewa mun zabi rana na musamman domin murnar demokradiyya, akwai takaici har yanzu mun gaza yiwa al'ummarmu hallaci."

A bangare guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya danganta kashe-kashen 'yan bindiga da kuma na mayakan Boko Haram da dokar kullen da aka saka a kasar nan sakamakon annobar Coronavirus.

Shugaban kasar wanda ya bayyana hakan yayin jawabi ga 'yan Najeriya a ranar Damokaradiyya, ya nuna damuwarsa a kan yadda rayukan jama'a ke salwanta sakamakon al'amuran 'yan ta'adda a fadin kasar nan.

Kamar yadda yace, gwamnatin sa ta fifita kawo karshen duk wani nau'i na rashin gaskiya kuma dakarun sojin kasar nan sun murkushesu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel