Zaben Edo: Obaseki ya yi martani kan korarsa daga takarar gwamna a APC

Zaben Edo: Obaseki ya yi martani kan korarsa daga takarar gwamna a APC

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi martani a kan sanarwar da kwamitin tantance yan takarar gwamnan na jamiyyar APC ta yi inda ta ce bai cika kaidojin shiga takarar ba.

Obaseki ya ce bai zai daukaka kara ba ko kai maganan gaba bisa korarsa daga cikin yan takarar da aka yi a zaben fidda gwani na jamiyyar da ake sa ran yi a watan Satumban wannan shekarar.

A sakon da ya fitar ta bakin kakakinsa, Crusoe Osagie, gwamnan ya ce tabbas ya ce yadda ake cin zarafin demokradiyya karkashin jagorancin kwamared Adams Oshiomhole a jami'yyarsa ta APC.

Zaben Edo: Obaseki ya yi martani kan korarsa daga takarar gwamna a APC
Zaben Edo: Obaseki ya yi martani kan korarsa daga takarar gwamna a APC
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki a Borno

Gwamnan ya ce wannan lamarin abin takaici ne da bacin rai.

Obaseki ya ce tun da farko ya san ba za ayi masa adalci ba duba da yadda mutum daya ke karya dokoki yana juya jami'yyar yadda ya ke so gabanin tantance 'yan takarar gwamnan na zaben Edo.

Obaseki ya cigaba da cewa abin kunya ne yadda "a fili ake cin zarafin demokradiyya, saba dokoki da rashin adalci" da Kwamared Adams Oshiomhole ya jawo a jami'yyar.

"Abin bakin ciki ne hakan ya rika faruwa a jamiyyar da ke ikirarin kawo canji da adalci," in ji shi.

"Domin haka mun yanke shawarar cewa bata lokaci ne daukaka wannan batun zuwa gaba a jami'yyar APC musamman tunda Oshiomhole ya bawa kansa wuka da nama yana aikata duk abinda ya ke so.

"Muna yi wa Oshiomhole fatan alheri a mulkinsa na rashin adalci kuma muna fatan Allah ya taimaki kasar mu ta gano hanyar gaskiya, 'yanci da adalci," a cewar Obaseki.

Ya kuma yi kira da 'ya'yan jami'yyar da dimbin magoya bayansa su kwantar da hankulansu su saurari matakan da za a dauka nan gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel