An kwato yankunan da 'yan ta'adda suka kwace, jama'a sun koma gidajensu - Buhari

An kwato yankunan da 'yan ta'adda suka kwace, jama'a sun koma gidajensu - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce an kwato dukkan kananan hukumomin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kwace a jihar Borno, Yobe da Adamawa.

A halin yanzu, dukkan 'yan gudun hijira da suka tsere sun koma yankunansu bayan samun zaman lafiya.

A jawabin da Buhari ya yi ga 'yan Najeriya a ranar tunawa da damokaradiyya ta 2020, ya ce: "Durkushewar da aka samu a wadannan yankunan wanda ya zama babbar barazana ga samuwar abinci a kasar nan duk sun zo karshe.

"An ci gaba da noma tare da sauran al'amuran tattalin arziki a yankunan."

Hakazalika, ya mika ta'azaiyyarsa ga mutanen jihohin Katsina da Borno da suka rasa rayukan 'yan uwansu sakamakon ayyukan 'yan bindiga wanda ya ce dokar kulle ta korona ce ta assasa.

Ya ce: "Hukumomin tsaro na kan bincike kuma za a tabbatar da adalci."

An kwato yankunan da 'yan ta'adda suka kwace, jama'a sun koma gidajensu - Buhari
An kwato yankunan da 'yan ta'adda suka kwace, jama'a sun koma gidajensu - Buhari. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ranar damokaradiyya: Abubuwa 10 da Buhari ya yayi magana a kansu

A wani labari na daban, a ranar Juma'a, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga 'yan Najeriya don tunawa da ranar damokaradiyya ta 2020.

Ya yi amfani da damar wurin bayyana ci gaban da aka samu a manyan sassa a fadin kasar nan. Buhari ya ce mulkinsa ya samu manyan ci gaba duk da ci baya da aka samu a wasu sassan.

Ga abubuwa 10 da shugaban kasa ya lissafa a cikin jawabinsa:

1. An kammala titi mai tsawon kilomita 412 da ke Sukuk.

2. Kara hanyoyin yalwatar tattarin aziki ta noma da kiwo ba dogaro da man fetur ba kadai.

3. An yi amfanin da ya dace da kudaden da shugabannin da suka gabata suka wawure ta yadda ya dace.

4. Kokarin shawo kan rashin tsaro: An nakasa mayakan Boko Haram tare da durkusar da su.

5. Nasarar ciyar da yaran makaranta miliyan 10 da sauran al'amura na walwala da more rayuwa.

6. Manyan nasarori na samuwa a bangaren wutar lantarkin kasar nan.

7. Ilimi kyauta kuma na dole ga dukkan kananan yara a fadin kasar nan.

8. 'Yancin kafafen yada labarai: Gwamnatin Buhari ta tabbatar da 'yancin manema labarai a dukkan kasar nan.

9. Kokarin kawo karshen annobar korona wacce ta bullo kasar nan a watan Fabrairu na shekarar nan.

10. Ana gab da kammala gada ta biyu ta Neja wacce ta dade ana aikinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel