Da ɗumi-ɗumi: APC ta kori Obaseki daga cikin 'yan takara kan wasu dalilai biyu

Da ɗumi-ɗumi: APC ta kori Obaseki daga cikin 'yan takara kan wasu dalilai biyu

Jami'yyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da hana gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki daga shiga zaben fidda gwani na takarar zaben gwamna da za a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.

Shugaban, kwamitin tantance yan takarar, Jonathan Ayuba ne ya bayar da sanarwar a sakatariyar jamiyyar da ke birnin tarayya Abuja yayin da ya ke mika rahoto ga kwamitin gudanarwa (NWC).

Ayuba ya ce an kori Obaseki daga takarar ne saboda ya gabatar da sakamakon kammala karatun sakandare mai matsala.

Kwamitin ta kuma ce akwai kuskure wurin rubuta sunan Obaseki a takardar shaidan kammala aikin yi wa kasa hidima, NYSC, da ya gabatar.

Wasu da aka hana shiga takarar sun hada da Engr. Chris Ogiemwonyi da Matthew Iduoriyekemewen.

DUBA WANNAN: An kama mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki a Borno

A kwanakin baya ne Gwamna Obaseki ya nuna damuwarsa game da kwamitin tantance yan takarar na APC da ya ce baya tsamanin za a yi masa adalci saboda rashin jituwarsa da shugaban jamiyyar na kasa Adams Oshiomhole.

Obaseki da Oshiomhole dai sun dade suna kai ruwa rana a jihar ta Edo inda kowa ke kokarin ganin shine ke juya akalar jamiyyar a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel