Kotu ta ba da umarnin tsare dan jaridar da ya zagi Lai Mohammed

Kotu ta ba da umarnin tsare dan jaridar da ya zagi Lai Mohammed

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Abuja, ta ba da umarnin tsare Rotimi Jolayemi, dan jaridar da aka kama da laifin caccakar Ministan Labarai da Al'adu na Najeriya, Lai Mohammed.

Yayin zartar da hukuncin a ranar Alhamis, Mai shari'a Anwuli Chikere, ya ba da umarnin tsare Jolayemi, inda kotun ke tuhumarsa da kalaman nuna kiyayya da cin mutuncin ministan kasar.

Kotun ta bukaci a tsare wanda ake tuhumar a reshen miyagun laifuka na hedikwatar 'yan sanda da ke Abuja gabanin ta saurari bukatar bayar da belinsa.

A yayin da Jolayemi ya koka kan rashin lafiya da ya ke fama da ita domin a ba da belinsa, kotun ta yi burus inda ta dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Yuni.

Lauyan Jolayemi, Soji Toki, bai yi wata jayayya a kan hukuncin da kotun ta zartar ba kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Jolayemi wanda ya jagoranci wani shiri mai taken ‘Bi aye se ri’ da aka yada cikin harshen Yarbanci, ya fada hannun jami’an tsaro ne bayan ya rera wani wake wanda ya soki ministan.

Dan jaridar ya shiga hannun jami'an tsaro tun a ranar 5 ga watan Mayu, biyo bayan yada wannan wake a gidajen rediyo na jihar Osun da Kwara wanda bai yi wa ministan dadi ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, jami'an tsaro sun cafke matar Jolayemi da kuma 'yan uwansa maza biyu inda suka shafe tsawon mako guda a daure bayan sun ki fadin inda dan jaridar ya ke.

Lai Mohammed, Jolayemi da matarsa
Hakkin mallakar hoto: Jaridar The Punch
Lai Mohammed, Jolayemi da matarsa Hakkin mallakar hoto: Jaridar The Punch
Asali: Twitter

Daga bisani an bari sun shaki iskar 'yanci bayan da Jolayemi ya mika kansa ga jami'an tsaro.

Jolayemi wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar 'yan jarida masu cin gashin kansu a Najeriya reshen jihar Osun, an garzaya da shi Abuja a ranar 7 ga watan Mayu inda aka ci gaba da tsare shi.

KARANTA KUMA: Wakar da ta sa Ministan Labarai, Lai Mohammed, ya ba da umarnin a kama dan jarida, Jolayemi

Legit.ng ta ruwaito cewa, Kungiyar kare hakkin bil Adama, Amnesty International, ta bukaci rundunar 'yan sandan Najeriya ta gaggauta sakin dan jarida da ta kama.

Amnesty ta bukaci a saki dan jaridar wanda a yanzu ya shafe tsawon makonni biyar tsare a hannu hukuma saboda kawai ya soki Ministan na Najeriya.

Da ta ke martani dangane da wannan keta haddin bil Adama, Amnesty cikin wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter, ta ce kama dan jaridar da matarsa ya saba wa shari'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel