Sau 19 yan Boko Haram suka kai hari Borno cikin watan nan - Kwamandan runduna

Sau 19 yan Boko Haram suka kai hari Borno cikin watan nan - Kwamandan runduna

Jihar Borno ta fuskanci munanan hare-hare akalla goma sha tara (19) daga wajen yan ta'addan Boko Haram cikin kwanaki goman farkon wannan watan Yunin da muke ciki.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin kwamandan hukumar tsaron farin kaya watau NSCDC na jihar Borno, Ibrahim Abdullahi.

Ya bayyana hakan ne yayinda yake hira da manema labarai ranar Alhamis inda aka nunawa duniya wasu yan baranda da suka shiga hannu. Amma bai bayyana ainihin wuraren da aka kai wadannan hare-hare ba.

A bisa binciken da Daily Trust ta gudanar, wadannan hare-hare 19 da aka kai basu hada da wadanda yan ta'addan ke kaiwa cikin kauyuka da ba'a samu ruwaitowa.

Yayin bayyanasu, kwamandan NSCDC ya ce yawaitan hare-haren Boko Haram ya wajabtawa hukumar da takwarorinta zange dantse wajen ayyukansu.

Daga cikin wadanda aka damke akwai wani dan aiken yan Boko Haram mai suna Bakura Ibrahim da aka damke.

Abdullahi ya ce Bakura Ibrahim ya shiga hannun jami'ai a garejin Muna da ke kan titin Gamboru Ngala da ke Maiduguri a ranar Asabar, 6 ga watan Yuni.

Sau 19 yan Boko Haram suka kai hari Borno cikin watan nan - Kwamandan runduna
Sau 19 yan Boko Haram
Source: Twitter

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun yiwa Soja da dan sanda kisan wulakanci a sabon faifan bidiyo

Legit ta ruwaito muku cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Laraba ya tabbatar da kisan mutane 81 da jana'izarsu sakamakon garin da yan ta'addan Boko Haram suka kai Arewacin jihar ranar Talata.

Zulum ya bayyana hakan ne rabar Laraba yayinda yake hira da manema labarai a garin Felo, karamar hukumar Gubio inda harin ya faru.

Bayan kisan mutane 69 a farko, yan ta'addan sun sake komawa suka bankawa gidajen wuta.

Jimamin gwamnan ya bayyana a muryarsa yayinda yake jawabin kan irin kisan gillar da ake yiwa al'ummarsa.

Ya kara tabbatar da rahoton cewa yan ta'addan sun yi awon gaba da mutane shida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel