'Yan Najeriya miliyan 39.4 na iya rasa ayyukansu kafin karshen shekara - FG

'Yan Najeriya miliyan 39.4 na iya rasa ayyukansu kafin karshen shekara - FG

Gwamnatin tarayyar ta yi bayyana cewa mudin ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, a kalla 'yan Najeriya miliyan 39.4 suna iya rasa ayyukansu sakamakon tsaikon da annobar COVID-19 ta yi a kasar.

Ta kuma bayyana fargabatar ta kan yiwuwar miliyoyin yan Najeriya za su fada cikin halin matsanancin talauci kafin annobar ta wuce.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya yi wannan jawabin a ranar Alhamis yayin da ya ke gabatar da jawabin kwamitin tattalin arziki ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

'Yan Najeriya miliyan 39.4 na iya rasa ayyukansu kafin karshen shekara - FG
'Yan Najeriya miliyan 39.4 na iya rasa ayyukansu kafin karshen shekara - FG. Hoto daga The Guardian
Asali: UGC

Buhari ya kafa kwamitin ne tun a ranar 30 ga watan Maris na 2020 a lokacin da ake ganin annobar coronavirus tana barazana ga tattalin arzikin kasar.

DUBA WANNAN: An kama mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki a Borno

An daura wa kwamitin nauyin binciko hanyoyin da Najeriya za ta bi domin tunkarar kallubalen da ke fuskantar kasar sakamakon annobar ta COVID-19.

A yayin da ya ke gabatar da rahoton ga Buhari, Osinbajo ya ce dokar kulle na bayar da tazara da aka saka don dakile yaduwar cutar sun bangarorin samun kudade kamar noma, kasuwanci, sufuri da yawon bude ido.

Ya ce akwai yiwuwar kudaden da ake ware wa bangarorin gwamnati uku duk wata zai ragu da Naira biliyan 185.

Osinbajo ya ce kwamitin ta bayar da shawarar kirkirar tsare tsare da za su samar wa mutane ayyuka da kuma yin amfani da kayayyakin cikin gida a maimakon sayo na kasashen waje.

Kwamitin ta kuma shawarci gwamnati ta fadada shirin rage talauci ta hanyar daukan sabbin yan N-Power da bawa kananan yan kasuwa bashi karkashin shirin MarketMoni da TraderMoni.

A karshe kwamitin ta bayar da shawarar ministoci su saka ido domin ganin an aiwatar da shirye shiryen da ke karkashin ma'aikatunsu domin samun nasara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel