EFCC na bincikar wasu gwamnoni da ke kan mulki – Magu

EFCC na bincikar wasu gwamnoni da ke kan mulki – Magu

Mukadashin Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa, EFCC, Ibrahim Magu ya ce Hukumar yaki da rashawar tana bincikar gwamnoni da ke kan mulki da wasu tsaffin gwamnoni da ake zargi da almundaha da kudade.

A cewarsa, ana gayyatar wadanda ake zargin sun hada baki da gwamnonin wurin aikata wawure kudaden gwamnati domin su amsa tambayoyi.

Amma, Magu bai bayyana sunayen gwamnonin da ake bincike a kansu ba inda ya ce hakan na iya janyo cikas ga binciken kamar yadda The Punch ta ruwaito.

EFCC na bincikar wasu gwamnoni da ke kan mulki – Magu
EFCC na bincikar wasu gwamnoni da ke kan mulki – Magu. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki a Borno

Da ya ke jawabi yayin taron manema labarai da aka kira domin murnar ranar demokradiya ta shekarar 2020 a Abuja, Magu ya ce hukumar ta EFCC ta kwato kadarori da kudinsa ya dara Naira biliyan 980 a shekaru biyar da suka shude.

Ya ce, "Muna samun nasara a binciken da muke gudanarwa, mun yi nasara a kotu a kan mutum 2,240 da muka gurfanar a cikin shekaru biyar da suka gabata. Mun kwato kadarori da kudinsu ya fi Naira biliyan 980 da tsabar kudade masu yawa.

"Muna kuma bincike a kan wasu gwamnoni da ke kan mulki da wasuu tsaffin gwamnoni, mun gayyatar wadanda suka hada baki da gwamnonin domin yi musu tambayoyi."

A wani labari da Legit.ng ta wallafa, Jami'an hukumar NSCDC a jihar Borno sun damke wani mutum da ake zargi da samar wa mayakan Boko Haram kayan bukata.

Kwamandan NSCDC na jihar Borno, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da hakan a garin Maiduguri a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni.

Ya ce an kama mutumin ne da mota dankare da man fetur tare da sauran kayan bukata.

Abdullahi ya ce wanda ake zargin mai suna Bakura Ibrahim ya shiga hannun jami'ai a garejin Muna da ke kan titin Gamboru Ngala da ke Maiduguri a ranar Asabar, 6 ga watan Yuni.

Kayayyakin da aka samu a wurin mutumin mai shekaru 35 sun hada da jarkoki 35 masu cin lita 25 cike da man fetur, kwalin magungunan gargajiya bakwai, jaka 10 ta koma da ragar kamun kifi sai kuma magungunan karin karfin maza.

Kwamandan ya kara da cewa, da hadin guiwar sauran jami'an tsaro sun samu manyan nasarori wurin yaki da barna.

Kwamandan ya ce hukumar ta yi nasarar damke manyan 'yan ta'addan Boko Haram uku tare da mika su ga rundunar soji don daukar mataki a 2020.

Ya danganta yawaitar hare-haren da 'yan ta'addan ke kaiwa da yawan masu samarwa 'yan ta'addan bayanai, kayan bukata da kuma masoyansu da ke zaune a cikin mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel