Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun yiwa Soja da dan sanda kisan wulakanci a sabon faifan bidiyo

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun yiwa Soja da dan sanda kisan wulakanci a sabon faifan bidiyo

Yan kungiyar daular Musulunci a yankin Afrika ta yamma wato ISWAP, wani balin Boko Haram sun saki bidiyon yadda suka yiwa wani Soja da dan sanda yankan rago.

A faifan bidiyon dakika 49 da Premium Times ta gani, yan Boko Haram suna kashe jami'an tsaron biyu ta hanyar bindigesu a tsanake.

An yi garkuwa da jami'an tsaron biyu ne makon da ya gabata yayinda suke hanyar tafiya tsakanin Maiduguri da Monguno a jihar Borno.

Gabanin kashesu, jami'an tsaron sun yi gajeren jawabi.

A cewar daya cikinsu, ya ce suna hanyar tafiya ne daga Maiduguri zuwa Monguno yayinda yan ta'addan suka bude musu wuta kuma sukayi garkuwa da su.

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun yiwa Soja da dan sanda kisan wulakanci a sabon faifan bidiyo
Yan Boko Haram
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kasashen Afrika 14 masu 'yan sanda mafi kwarewa a kan aiki

Na farkon wanda yayi magana a harshen Hausa yace: "Suna na Yohana Kilu, ni dan sanda ne mai mukamin Sifeto, an yi garkuwa da ni tsakanin Maiduguri da Monguno; yanzu hakan ina hannun Sojojin Tilafa."

Na biyun yace: "Ni 13NA/70/8374, Lance Corporal Emmanuel Oscar, yan Tilafa sun yi garkuwa da ni a hanyar Maiduguri zuwa Monguno."

Bayan jawabinsu, bidiyon ya nuna yadda wasu yan bindiga biyu suka shirya bindige jami'an tsaron biyu bayan rufe musu idanu. kawai sai suka harbesu.

Har yanzu ba'a san takamamman lokacin da aka dauki bidiyon ba amma an saki bidiyon ne kwanaki uku bayan harin Boko Haram na karamar hukumar Gubio da aka hallaka mutane akalla 81.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel