Da ɗumi-ɗumi: An samu karin masu korona 681, jimilla 14,554

Da ɗumi-ɗumi: An samu karin masu korona 681, jimilla 14,554

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 681 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.48 na daren ranar Alhamis 11 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 681 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Lagos-345

Rivers-51

Ogun-48

Gombe-47

Oyo-36

Imo-31

Delta-28

Kano-23

DUBA WANNAN: An kama mai kaiwa 'yan Boko Haram kayan aiki a Borno

Bauchi-18

Edo-12

Katsina-12

Kaduna-9

Anambra-7

Jigawa-5

Kebbi-4

Ondo-4

Nasarawa-1

Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Alhamis 11 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 14554.

An sallami mutum 4494 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 387.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da yasa ba lallai ta kara saka dokar kulle a kasa saboda hauhawar masu kamuwa da annobar korona ba.

Shugaban kwamitin kar ta kwana a kan korona (PTF), kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin taron hadin gwuiwa da kwamitin PTF ya saba gudanarwa.

"Kamar yadda na fada a baya, zamu sake duba na tsanaki a kan yanayin da ake ciki. Duk matakin da zamu dauka a nan gaba zai kasance bisa shawarar masana da kwararru a bangaren kimiyya da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

"Sannan dole mu duba halin da gwamnatinmu ke ciki, mu duba irin nasarorin da muke son cimma da kuma sake duban abubuwan da suka faru a tsawon sati biyar da aka yi a cikin dokar kulle," a cewar Boss Mustapha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel