Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi ranar Juma'a

Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi ranar Juma'a

Shugaba Muhammadu Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi gobe Talata, 12 ga watan Yuni, 2020 misalin karfe 7 na safe.

Buhari zai yi jawabin ne domin murnar ranar Demokradiyya.

Hadimin Buhari kan kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Yace: "Domin murnar ranar Demokradiyyan Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga yan Najeriya ranar Juma'a, 12 ga Yuni, 2020 misalin karfe 7 na safe."

"Ana kira ga gidajen talabijin da rediyo su yi tarayya a tashar NTA da FRCN."

KU KARANTA: A taimaka mana yunwa zata kashe mu - Malaman makarantun kudi sun koka

Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi ranar Juma'a
Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi ranar Juma'a
Asali: Facebook

Shekarun baya, an saba gudanar da bikin ranar dimokuradiya a ranar 29 ga watan Mayu na kowace shekara gabanin shugaba Buhari ya sauya ranar a shekarar 2018.

Buhari ya yi hakan ne domin karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar ta GCFR, domin tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Legit ta kawo muku rahoton cewa gwamnatin tarayyar Najeriya, ta ayyana ranar Juma'a, 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar hutun aiki domin gudanar da bikin ranar Dimokuradiyya ta wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya ayyana ranar hutun a madadin gwamnatin tarayyar kasar.

Ya na mai taya daukacin al'ummar Najeriya na nan gida da kuma wadanda suke ketare, murnar zagayowar wannan rana da aka sauya salon mulki daga hannu soji ya koma hannun farar hula.

Ministan ya jinjinawa gwarazan mutanen da suka taka rawar gani wajen sadaukarwar da ta tabbatar da komawa kan tsarin mulki na Dimokuradiya a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel