Coronavirus: Osinbajo ya gabatar da tsare-tsaren yadda Najeriya za ta farfado da tattalin arziki

Coronavirus: Osinbajo ya gabatar da tsare-tsaren yadda Najeriya za ta farfado da tattalin arziki

A ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya gabatar wa da shugaba Muhammadu Buhari rahoton farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Osinbajo wanda ya kasance jagoran kwamitin kula da tattalin arzikin Najeriya, ya gabatar da manufofi da za su ba da damarbullo da dabarun farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Ana iya tuna cewa, tun a ranar 30 ga watan Maris, Buhari ya kaddamar da kwamitin kula da tattalin arziki a yayin da annobar korona ta yi wa dukkanin kasashen duniya shigar ba zata.

Babu shakka mummunan tasiri musamman na karayar tattalin arziki da annobar korona ta janyo ba a taba fuskantar makamancinsa ba tsawon shekaru 80 gabata a tarihi kamar yadda alkaluma suka nuna.

Da ya gabatar da rahoton a fadar shugaban kasa, Osinbajo ya ce kwamitin ya bijiro da wasu matakai da za su mayar da annobar korona wata dama ta farfado da tattalin arzikin kasar.

Jigo cikin matakan shi ne shimfida tsare-tsaren samar da ayyukan yi domin tunkarar kalubalen da annobar korona ta haddasa.

Osinbajo yayin gabatar da tsare-tsaren yadda Najeriya za ta farfado da tattalin arziki
Hakkin mallakar Hoto: Fadar shugaban kasa
Osinbajo yayin gabatar da tsare-tsaren yadda Najeriya za ta farfado da tattalin arziki Hakkin mallakar Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

Osinbajo yana mai ba da shawarar cewa, dole sai gwamnati ta mike tsaye tare da zage dantse wajen samar da ayyukan yi domin kawar da mummunan tasirin da annobar korona ta haifar.

Daga cikin matakan samar da aikin yi da mataimakin shugaban kasar ya gabatar a rahotonsa, ya shawarci gwamnati ta mayar da hankali kan sha'anin noma a duk jihohin da ke tarayyar kasar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, Osinbajo ya nemi gwamnatin ta ba da himma wajen fadada shirin gine-ginen tintuna, manya da kanana a cikin birane da karkara.

KARANTA KUMA: Majalisa ta amince da kasafin kudin 2020 da aka yi wa kwaskwarima

Sai kuma shirin gine-ginen mahalli domin samar da akalla gidaje 300,000 a duk shekara, inda ƙwararrun matasa da masu fasahar sana'o'in hannu za su samu abin yi.

Mataimakin shugaban kasar ya yi gargadin cewa, muddin ba a farga ba, rashin aikin yi a kasar na iya karuwa da kashi 33.6 cikin dari.

Ya ce matukar ba a dauki matakan da suka dace ba, to kuwa akwai yiwuwar kimanin mutane miliyan 39.4 za su iya rasa ayyukansu daga yanzu zuwa karshen shekarar 2020.

A nasa jawaban yayin karbar rahoton, shugaba Buhari ya yabawa kawaicin da 'yan Najeriya suka yi da kuma jajircewarsu wajen riko da kaddarar da ke tattare da annobar korona.

Yayin da cutar korona ke ci gaba da kutsawa cikin duk wani kwararo da sako, Buhari ya ce a yanzu babu wani tattalin arziki da cutar ba ta yi wa illa ba a fadin duniya komai karfinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel