Da duminsa: Majalisar dattawa ta tabbatar da sabbin jakadu 42 (Jerin sunayensu)
Majalisar dattawa a ranar Alhamis ta amince da mutane 42 da shugaban Buhari ya zaba matsayin sabbin jakadun Najeriya zuwa kasashen waje.
Hakazalika majalisar ta amince da nadin Justice Monica Dongban-Mensem a matsayin shugabar kotun daukaka kara da kuma James Kolo matsayin kwamishana a hukumar FCC.
Tabbatar da su ya biyo bayan rahoton kwamitin Sanata Adamu Bulkachuwa wanda shine shugaban kwamitin harkokin waje a majalisar dattawa.
Za ku tuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya aike da sunayen mutane 42 da ya zaba matsayin jakadun Najeriya.

Asali: UGC
KU KARANTA: Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi ranar Juma'a
Ga jerin sunayen wadanda aka tabbatar:
Innocent Alaoma Iwejuo
Aishatu Aliyu Iwejuo
Mukhtar Ibrahim Bashir
Chikezie Ogbonna Nwachukwu
Alex Enan Kefas
Gabriel Mustapha Okoko
Aisha Mohammed Garba
Asari Edem Allotey (Mrs.)
George Ehidiamen Edokpa, Esq
Adamu Ibrahim Lamuwa
Abubakar Mohammed Sarki
Yakubu Abdullahi Ahmed
Suleiman Dauda Umar
Gambo Yusuf Hamza
Nura Abba Rimi
Mfawa Omini Abam
Lami Sauda Remawa-Ahmed
Mohammed Manu
Ingekem Regina Ocheni (Mrs.)
Ismaila Yusuf Abba
Mistura Abdulraheem (Mrs.)
Wosilat Abimbola Adedeji
Obinna Cheedu Onowu
Ekpebike Steve Agnana
Ogah Usman Ari
Safiu Olukayode Olaniyan
Abidoun Richards Adejola
Olawale Emmanuel Awe
Ibim Nkem Charles
Zachariah Mallam Ifu
Raymond Udoffe Brown
Godfrey A. E. Odudigbo
Ahmed Sule
Olukayode O. Aluko
Victor Adekunle Adeleke, Esq
Matin Senkom Adamu
Bukar Buni Hamman
Anderson Nkemakonam Mabubike
Nart Augustine Kolo,
Ismail Ayobami Alatishe
Yakubu Santuraki Suleiman
Benaoyagha Bernard Mese Okoyen
A bangare guda, Legit ta ruwaito muku cewa Majalisar dattawa ta yi barazanar bayar da sammacin kama Ministan Labarai da Al’adu; Alhaji Lai Mohammed, Karamin Ministan Man Fetur; Timipre Sylva da kuma Ministan Wuta; Engr. Saleh Mamman.
Majalisar ta ce za ta bayar da sammacin cafke ministocin uku saboda sun ki amsa goron gayyatar da ta ba su na neman su yi bayani a kan duk wani shige-da-fice na batar da kudi a ma'aikatunsu.
Shugaban kwamitin kula da kudin al'umma a majalisar, Sanata Matthew Urhoghide na jam'iyyar PDP mai wakiltar shiyar Edo ta Kudu, shi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng