Anyi garkuwa da babban yayan tsohon gwamna Murtala Nyako mai shekaru 90

Anyi garkuwa da babban yayan tsohon gwamna Murtala Nyako mai shekaru 90

Hukumar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da labarin garkuwa da Alhaji Dahiru Nyako, dattijo dan shekara 90 kuma babban yayan tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai NAN ranar Alhamis a garin Yola.

Nguroje ya ce wasu masu garkuwa da mutane ne sukayi awon gaba da shi misalin karfe 2 na daren Alhamis a gidansa dake cikin garin karamar hukumar Mayo-Belwa.

Nguroje yace: "Tuni hukumar ta tura jami'an yaki da garkuwa da mutane da dakarun Operation Farauta domin cetoshi."

Kananan hukumomin Mayo-Belwa, Jada, Ganye da Tongo dake yankin kudancin Adamawa sun dade suna fuskantar barazanar masu garkuwa da mutane da yan bindiga.

KU KARANTA: A taimaka mana yunwa zata kashe mu - Malaman makarantun kudi sun koka

Anyi garkuwa da babban yayan tsohon gwamna Murtala Nyako mai shekaru 90
Tsohon gwamna Murtala Nyako
Asali: Facebook

A bangare guda, Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Allah ya yiwa babban sakataren gudanarwa na kungiyar Jama'atu Izalatul bidi'a wa ikamatus sunnah (JIBWIS), Malam Mukhari Ibrahim (Vom) rasuwa.

Malam Mukhari Ibrahim ya kasance babban jami'i a kungiyar Izalah tun kafuwarta zuwa yanzu.

Legit.ng ta samu rahoton daga shafin kungiyar Jibwis na Facebook inda aka bayyana lokacin da za'ayi Sallar Jana'izarsa a jihar Bauchi.

Ga abinda jawabin yace: "Allah ya yiwa Malam Mukhari Ibrahim (Vom) Rasuwa. Malam Mukhtari shine Babban Admin Secretary na kungiyar IZALA tun farkon kafa kungiyar har zuwa lokacin rasuwar sa.

Za'a gabatar da sallar janaizar sa a masallacin Juma'ah na JIBWIS dake Gwallaga a cikin garin Bauchi da misalin karfe daya na rana 1:00pm a gobe Alhamis insha Allah, kamar yadda mataimakin shugaban JIBWIS na kasa, Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe ya sanar.

Allah Ubangiji ya gafarta masa yasa aljannar firdausi ne makomarsa da sauran musulmai muminai wadanda suka rigaye mu. Amin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel