Yanzu-yanzu: Ana baiwa hammata iska a majalisar dokokin jihar Kaduna (Bidiyo)
Mambobin majalisar dokokin jihar Kaduna su 24 sun tsige mataimakin kakakin majalisar, Hon. Mukhtar Isa Hazo.
Lamarin ya biyo bayan wani zabe da aka yi na rashin gamsuwa da shi.
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, ba a san takamaiman zargin da ake yi wa tsigaggen mataimakin kakakin majalisar ba.
Ba tare da bata lokaci ba aka nada sabon mataimakin kakakin domin ya maye gurbinsa kuma a cigaba da zama.

Asali: Twitter
Yan mintuna bayan nada Hanarabul Isaac Auta, sabon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, rikici ya kaure a zauren majalisar, bidiyon The Nation ya nuna.
An fara rikici ne yayinda dan majalisa mai wakiltan mazabar Makera, Hanarabul Liman Dahiru, ya shigo cikin zauren majalisa ya dauke sandar majalisa.
Yanzu haka ana ta fafatawa kan sandar majalisar.
Kalli bidiyon:
KU KARANTA: A taimaka mana yunwa zata kashe mu - Malaman makarantun kudi sun koka
Wannan na faruwa ne watanni uku bayan kokarin tsige kakakin majalisar dokokin Kaduna da mataimakinsa.
A ranar Talata, 25 ga Febrairu, 2020 yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun zabi Hanarabul Yusuf Ibrahim Zailani matsayin sabon kakakin majalisar.
An zabeshi ne kimanin awa daya bayan Hanarabul Aminu Abdullahi Shagali ya yi murabus daga kujerar.
Hanarabul Yusuf Ibrahim Zailani wanda ke wakiltar mazabar Igabi ta yamma, ya kasance mataimakin kakain majalisar kafin aka zabesa matsayin Kakaki a ranar Talata.
Zailani babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne a jihar Kaduna.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng