Allah ya yiwa babban sakataren Izalah, Malam Mukhari Ibrahim rasuwa
Inna liLLAHI wa inna ilaiHI rajii'un
Allah ya yiwa babban sakataren gudanarwa na kungiyar Jama'atu Izalatul bidi'a wa ikamatus sunnah (JIBWIS), Malam Mukhari Ibrahim rasuwa.
Malam Mukhari Ibrahim ya kasance babban jami'i a kungiyar Izalah tun kafuwarta zuwa yanzu.
Legit.ng ta samu rahoton daga shafin kungiyar Jibwis na Facebook inda aka bayyana lokacin da za'ayi Sallar Jana'izarsa a jihar Bauchi.

Asali: Facebook
KU KARANTA: A taimaka mana yunwa zata kashe mu - Malaman makarantun kudi sun koka
Ga abinda jawabin yace: "Allah ya yiwa Malam Mukhari Ibrahim (Vom) Rasuwa. Malam Mukhtari shine Babban Admin Secretary na kungiyar IZALA tun farkon kafa kungiyar har zuwa lokacin rasuwar sa.
Za'a gabatar da sallar janaizar sa a masallacin Juma'ah na JIBWIS dake Gwallaga a cikin garin Bauchi da misalin karfe daya na rana 1:00pm a gobe Alhamis insha Allah, kamar yadda mataimakin shugaban JIBWIS na kasa, Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe ya sanar.
Allah Ubangiji ya gafarta masa yasa aljannar firdausi ne makomarsa da sauran musulmai muminai wadanda suka rigaye mu. Amin."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng