A taimaka mana yunwa zata kashe mu - Malaman makarantun kudi sun koka

A taimaka mana yunwa zata kashe mu - Malaman makarantun kudi sun koka

Malaman makarantun kudi sun yi kira ga gwamnati ta taimaka musu da tallafi saboda cigaba da kulle makarantu sakamakon annobar cutar Korona ya saka su cikin halin kakanikaye.

Malaman sun ce yunwa na kan halakasu saboda yawancin makarantun da suke koyarwa sun ki biyansu albashi.

A jawabin da kakakin kungiyar Malaman, AbdulGaniy Raji, ya fitar, kuma ya aikewa jaridar Tribune a Kaduna, malaman makarantun kudin sun ce gaskiya gwamnati batayi adalci ba idan ta bari yunwa ta hallakasu kafin kawo musu dauki.

Yace: "Ba zai yiwu a cigaba da ko-oho da jin dadin malaman makarantun kudi ba. Yanzu cikin halin yunwa suke."

"Ya kamata mu tuna cewa malaman makarantun kudi na rayuwa ne kan kudin da suke samu daga kwastamomi (iyaye) kuma yanzu mun san iyaye basu biya kudin makarantar zango na uku ba."

"Dukkan hanyoyin da kudi ke shigowa makarantun kudi a toshe yake sakamakon dokar kullen nan. Gwamnati ta taimaka ta motsa kan lamarin makarantun kudi."

A taimaka mana yunwa zata kashe mu - Malaman makarantun kudi sun koka
Malaman makarantun kudi sun koka
Asali: Depositphotos

Kungiyar ta kara da cewa tsawon watanni biyu yanzu, makarantu na kulle bisa ga biyayya ga umurnin kullesu da gwamnatin tarayya tayi don takaita yaduwar cutar Coronavirus.

"Shin tun lokacin da aka fara dokar kullen nan, babu wanda yake tunanin yadda masu makarantun kudi ke fama da albashin malamansu?

"Shin babu wanda ya damu ya tattauna da su kan yadda za'a taimakawa iyalansu?"

"A jihar Legas, an kulle makarantu tun watan Maris. Yanzu muna Yuni, shin an san akwai makarantun da basu biya albashin Maris da Afrilu ba kuwa?

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu ranar bude makarantun Boko da na Islamiyya saboda tsoron yaduwar cutar Coronavirus cikin daliban makaranta.

Kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki ta cutar COVID-19 ta bayyana hakan a hira da manema labarai a Abuja.

Amma da alamu jihohin Borno da Corss River na shirin bude makarantunsu saboda dalibai su koma karatu.

Yayinda gwamnan jihar Corss River, Ben Ayade, ya bayyana cewa za'a bude makarantu ranar 16 ga Yuni, gwamnan jihar Borno, Farfesa Umara Zulum ya bude makarantu a karamar hukumar Bama kadai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel