Wata bakuwar cuta ta kashe shanu da dama a jihar Kano

Wata bakuwar cuta ta kashe shanu da dama a jihar Kano

Mun samu rahoton cewa, bullar wata bakuwar cutar dabbobi ta kashe shanu masu yawa a jihar Kano.

Cutar wadda ake kira Contagious Bovine Pleuropneumonia (CBPP), ta janyo asarar shanu da dama a jihar Kano kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Shugaban kungiyar masu kiwon dabbobi ta Dairy and Livestock Husbandry Cooperative Union, Usman Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Asabar.

CBPP cuta ce wadda ke addabar shanu da kuma ɓauna. Ta na yi wa hunhu da sauran kafofin fitar numfashi na jikin dabbobi lahani.

A yayin da wasu kwayoyin halittu na bakteriya da ake kira Mycoplasma mycoides ke janyo cutar, ta na haddasawa dabbobi zazzabi, tari, da fitar majina.

Wata bakuwar cuta ta kashe shanu da dama a jihar Kano
Wata bakuwar cuta ta kashe shanu da dama a jihar Kano
Asali: UGC

Cutar ta na harbin dabbobi yayin da aka samu cudanya tsakanin masu lafiya da masu dauke da kwayoyin cutar.

Tarihin ya tabbatar da cewa, a shekarar 1924 shi ne karo na farko da aka samu bullar cutar a Najeriya.

Kiyasi ya nuna cewa a tsakanin shekarar 1924 zuwa 1960, cutar ta hallaka shanu 200 a kowace shekara musamman a lardunan jihar Borno da Kano da ke Arewacin Najeriya.

KARANTA KUMA: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa

Rahotanni sun bayyana cewa, an shawo kan cutar a Najeriya a shekarar 1965, sai kuma daga bisani ta sake bulla.

Mallam Usman ya bayyana cewa, a cikin makonni biyu kacal, bakuwar cutar ta kashe shanu 100 a rugar Fulani da ke karamar hukumar Bunkure ta jihar Kano.

Ya ce hakan ya faru a lokacin da aka shimfida dokar kulle a watan Maris, inda lamarin ya kara tsananta a tsakanin watan Afrilu zuwa Mayu.

“Akwai manomi da ya rasa shanu 17, wasu sun rasa 20 yayin da kuma wasu sun rasa biyar.

"Amma babban abin bakin cikin shi ne yadda wani manomi ya yi asarar kusan shanu 50 cikin kankanin lokaci a karamar hukumar Bunkure ta jihar."

Ya ci gaba da cewa, annobar ta fara barkewa a tsakanin watan Nuwamba na shekarar 2019 zuwa Janairu na wannan shekarar.

A yayin da ake ci gaba da jiran tsammanin riga-kafin wannan cuta, Mallam Usman ya ce za a iya shafe tsawon shekara guda kafin a iya ganin bayanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel