Yanzu-yanzu: Gwamna Sule ya naɗa ƙanin IGP a matsayin sakataren gwamnatinsa

Yanzu-yanzu: Gwamna Sule ya naɗa ƙanin IGP a matsayin sakataren gwamnatinsa

- Gwamna Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya nada Barrister Mohammed Ubandoma Aliyu a matsayin sabon sakataren gwamnatinsa

- Ubandoma Aliyu kani ne ga Sufeta Janar na Rundunar Yan sandan Najeriya, Abubakar Adamu

- Gwamna Sule ya nada Ubandoma Aliyu ne don maye gurbin Ahmed Tijjani da aka sallama daga aiki bayan samunsa da laifin bannatar kudaden gwamnati

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya nada kanin Sufeta Janar na Yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, Barrister Mohammed Ubandoma Aliyu a matsayin sakataren gwamnatin jiharsa.

Mai magana da yawun gwamnan, Yakubu Lamai ne ya tabbatar da nadin cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A ranar Talata ne gwamnan ya tube tsohon SSG din, Alhaji Aliyu Ahmed Tijjani.

DUBA WANNAN Matawalle ya bawa tsohon ɗan takarar gwamnan APGA muhimmin muƙami

Kwamitin binciken da Majalisar Jihar ta kafa domin binciken yadda aka fitar da kudi Naira biliyan 1 domin gyara da gina katanga a makarantun gwamnati da ke jihar a 2018 sun samu tsohon SSG din da laifi.

Bayan samunsa da laifi, Yan majalisar jihar sun bukaco Ahmed Tijani ya dawo da fiye da Naira miliyan 248.5 da ba a san inda suka shige ba zuwa asusun gwamnatin jihar.

Majalisar ta ce tsohon kwamishinan ilimin ya nuna gazawa da rashin sanin makamashin aiki yayin gudanar da ayyukansa hakan yasa suke shawarci gwamnan ya sallame shi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Adamu dan asalin garin Lafia a matsayin Sufeta Janar na Yan sanda ne a ranar 15 ga watan Janairun 2019 don maye gurbin Ibrahim Kpotun Idris daga jihar Niger.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel