An kama masu hakar kabari da ke datse kawunan gawarwaki

An kama masu hakar kabari da ke datse kawunan gawarwaki

Wata kotun gargajiya da ke zamanta a Akure a jihar Ondo a ranar Laraba da bayar da umurnin 'yan sanda su cigaba da tsare wasu mutane biyu da aka kama da kawunnan 'yan adam.

Yan sanda sun kama wadanda ake zargin, Adewale Abiodun da Abel Olomofe da ke aiki a makabarta a karamar hukumar Akure ya Kudu.

Ana zarginsu da hako gawarwarki daga kaburbura suna datse musu kawunna a makabartar da ke Imafon Road a Akure.

An kama masu hakin kabari da ke datse kawunan gawarwaki
An kama masu hakin kabari da ke datse kawunan gawarwaki
Asali: UGC

An gurfanar da su ne a kotun bisa tuhuman su da aikata laifuka uku da suka shafi hadin baki, mallakar sassan jiki ba bisa kaida ba da cin zarafin gawa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamna Sule ya naɗa ƙanin IGP a matsayin sakataren gwamnatinsa

Laifukan sun ci karo da sashi na 516, 329 da 242 na dokar masu laifi na jihar Ondo ta shekarar 2006.

Dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Uloh Goodluck ya roki kotu ta bashi damar mika takardun bayannan binciken da ya yi ga ofishin direktan shari'ar na jihar domin samun shawara.

Lauyoyin da suke kare wadanda ake kara, Femi Adetoye da Jide Agboola sun roki kotun ta bayar da su a hannun beli.

A yayin yanke hukunci, Shugaban kotun, Tope Aladejana bai amince da bayar da belin ba kuma ya umurci wanda ya shigar da karar ya mika takardan bayanan zuwa ofishin direktan sharia bayan hakan sai a duba batun bayar da beli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel