Yan sanda sun bindige barawo yayinda yake kokarin guduwa da N3.5m da ya sace

Yan sanda sun bindige barawo yayinda yake kokarin guduwa da N3.5m da ya sace

Jami’an hukumar yan sanda a jihar Anambara sun bindige wani mutumi wanda ake zargi da laifin kwace jakar wani mai dauke da N3.5m, kusa da wani banki a garin Awka.

Wani mai idon shaida ya bayyanawa Punch Metro cewa barawon mai suna Chukwuemeka yayi musayar wuta da yan sanda na awanni yayinda yake kokarin guduwa da kudin.

"Yana ta harbi kawai. Ya harbe mutane hudu a musayar wuta. Amma yan sanda sun dakile shi, saboda ya samu raunuka a musayar wutan," wani mai idon shaida da aka sakaye sunansa ya laburta.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ya ce an damke barawon kuma an kwace makaminsa da kudin da ya sace.

KU KARANTA: Gwamnatin kasar Jamus ta baiwa Najeriya gudunmuwar €26m (N11.3bn)

Yan sanda sun bindige barawo yayinda yake kokarin guduwa da N3.5m da ya sace
Credit: Punch
Asali: Twitter

Mohammmed yace: “ Jami’an yan sandan dake tashar Regina na kusa da bankin Zenith a Awka sun samu kiran gaggawa cewa wani dan bindiga yana harbin kan mai uwa da wabi bayan kwace jakar kudi N3.5m daga hannun wani Ebuka Ukeakpu.”

“Dan bindigan, Chukwuemema, dan asalin karamar hukumar Akpoga Nkanu na jihar Enugu, ya tsallake rijiya da baya a yayinda matasa sukayi kokarin hallakashi kafin yan sanda suka ceceshi, suka kwace bindigar daga hannunsa da kudin da ya kwace.”

“ Mutane hudu sun raunata sakamakon harbin da ya rika yi, amma ba rauni mai hadari bane.”

Mohammed yace tuni an garzaya da su asibitin yan sanda dake Awka yayinda shi kuma barawon da yaci mugun duka hannun matasa na farfadowa.

Ya kara da cewa bayan kammala bincike kan lamarin za a garzaya dashi gaban kotun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel