Allah ya yi wa hadimin Aisha Buhari rasuwa

Allah ya yi wa hadimin Aisha Buhari rasuwa

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu ta rasa hadiminta mai suna Sani Yekini

- Kamar yadda ta bayyana, ya yi aiki a ofishinta na tsawon shekaru hudu kuma ya gwada kwazonsa

- Ta yi addu'ar samun rahama ga mamacin tare da hakurin jure babban rashin ga iyalansa

A ranar Laraba ne Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari, ta rasa hadiminta mai suna Sani Yekini.

Aisha ta sanar da mutuwar Yekini ta shafukanta na sada zumuntar zamani inda ta kwatanta shi da jajirtacce, mai kwazo da kuma kwarin guiwa.

Kamar yadda tace, marigayin ya yi aiki a karkashinta na shekaru hudu duk da ciwon sukari na damunsa.

DUBA WANNAN: Matawalle ya bawa tsohon ɗan takarar gwamnan APGA muhimmin muƙami

A yayin jaje ga iyalan mamacin, ta rubuta, "A madadain iyalai da dukkan ma'aikatan ofishina, ina mika ta'aziyyata ga iyalan Sani Yekin wanda ya rasu a ranar Laraba. Allah ya yarje masa Jannatul Firdaus.

"Yekini ya yi aiki a ofishina na tsawon shekaru hudu amma ciwon sukari ya kwantar da shi.

"Mutum ne mai mayar sa hankali, jajircewa da kwarin guiwa. Allah ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel