Ina matukar godiya - Ali Nuhu ya godewa masoya bisa ta'azziyar rashin mahaifinsa
Shahrarren Dan wasan kwaikwayo, Ali Muhammad Nuhu, ya mika godiyarsa ga ilahirin masoya da abokan arzikin da suka aika masa sakon ta'azziyar rashin mahaifinsa.
Ali Nuhu ya bayyana hakan ne a shafukansa na soshiyar Midiya.
Yace: "Ni da yan'uwana muna mika sakon godiya ga dukkan wadanda suka yi Mana ta'aziyyar mahaifinmu da ya rasu.Mungode Allah ya saka da alheri. Na gode da soyayya da kaunar da na samu daga gareku gaba daya, Allah ya bar zumunci."
An sanar da mutuwar mahaifin Ali Nuhu, Nuhu Poloma, ne ranar Talata, 8 ga watan Yuni, 2020 a shafin Instagram.
Daga cikin wadanda suka daura sune frodusa Nazoru Auwal Danhajiya da Maryam Booth.
Daga cikin wadanda suka aika masa sakon ta'aziyya sune dirakta janar na kamfanin raba wutanr lantarkin Kano, Dr Jamil Isyaku Gwamna.
Jamil Gwamna ya siffanta mutuwar Nuhu Paloma a matsayin babban rashi ga jihar Gombe.
A cewarsa, Mahaifin Ali Nuhu ya kasance babban dan siyasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin cigaban jihar.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya sake shan kaye a kotu
Duk a jiya Talatan, an yi asarar rayukan da dama a Arewacin Najeriya musamman jihohin Kastina da Borno.
Yayinda yan ta'addan Boko Haram suka kai hari karamar hukumar Gubio kuma suka hallaka akalla rayuka 81, yan bindiga sun kai mumunan farmaki karamar hukumar Faskati ta jihar Katsina inda suka hallaka rayuka 50.

Asali: UGC
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng