Kasashen Afrika 14 masu 'yan sanda mafi kwarewa a kan aiki

Kasashen Afrika 14 masu 'yan sanda mafi kwarewa a kan aiki

- Najeriya ba ta cikin sahun kasashen Afrika 14 mafi ingantacciyar rundunar 'yan sanda

- Kasar Bostwana ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka ta fuskar kwararriyar rundunar 'yan sanda

- Tunisia, Masar da Burkina Faso su na cikin jerin kasashen nahiyar Afrika da aka yaba da kwarewar 'yan sandansu

- Hakazalika ba'a bar kasar Ghana, Sudan, Rwanda da kuma Mali baya ba

A kididdigar da Hukumar Kula da Sha'anin Tsaro da 'Yan sanda ta Duniya, World Internal Security and Police Index (WISPI) ta fitar, rundunar 'yan sandan kasar Bostwana ta fi kowace kwarewa a nahiyar Afrika.

A cewar WISPI, kasar Bostwana ce a kan sahu na farko a fannin sha'anin kwarewar rundunar 'yan sanda cikin kowace kasa a nahiyar Afrika.

A rahoton da WISPI ta fitar, ta yi amfani da binciken da Dr. Mamdooh Abdelmottlep ya gudanar kan rundunar 'yan sandan duk kasashen duniya.

Dr. Abdelmottlep wanda Farfesa ne kan sha'anin tsaro, shi ne shugaban kungiyar nazari kan jami'an 'yan sanda ta duniya, International Police Science Association.

Jami'an 'Yan sandan kasashen Afrika
Jami'an 'Yan sandan kasashen Afrika
Asali: UGC

A wani sako da Africa Facts Zone ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Litinin, 8 ga watan Yuni, ta fitar da jerin kasashen nahiyar Afrika mafi ingantattun rundunar 'yan sanda.

Kasar Rwanda ce ta zo a mataki na biyu yayin da Algeriya ta biyo bayanta a mataki na uku cikin jerin kasashen 14.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Jihar Kano ta samu sabbin cibiyoyin gwaji guda 2

Ghana ta yi kane-kane a mataki na 8, yayin kasar Afrika ta Kudu, Morocco da Mali suka tirje a mataki na 9, 10 da kuma 11 a jere da juna.

Duk da kimarta da ake gani da kasancewarta madubin dubawa sanadiyar girman tattalin arzikinta da ya dara na kowace kasa a nahiyar, Najeriya ba ta samu shiga cikin jerin ba.

Ga dai Jerin Kasashe 14 mafi kwararrun 'Yan sanda a nahiyar Afrika kamar haka:

1. Botswana

2. Rwanda

3. Algeria

4. Senegal

5. Tunisia

6. Masar

7. Burkina Faso

8. Ghana

9. Afrika ta Kudu

10. Morocco

11. Mali

12. Sudan

13. Malawi

14. Burundi

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel