Yanzu-yanzu: Mataimakiyar shugaban bankin AfDB, Blanke ta yi murabus

Yanzu-yanzu: Mataimakiyar shugaban bankin AfDB, Blanke ta yi murabus

Mataimakiyar shugaban Bankin Bunkasa Tattalin Arzikin Afrika, AfDB, Dr Jennifer Blanke ta yi murabus daga aikinta kamar yadda bankin ta sanar a shafinta na Twitter.

Bankin ta bayyana hakan cikin sanarwar da ta fitar a ranar Laraba inda ta ce murabus din na Blanke zai fara aiki daga ranar 4 ga watan Yulin 2020.

An ruwaito ta ce, "Na ajiye aiki na ne domin in koma wurin iyali ne a Switzerland. Zan yi kewar bankin da kwararrun ma'aikatan da muka da shi. Zan cigaba da goyon bayan bankin daga duk inda na ke.

DUBA WANNAN: Matawalle ya bawa tsohon ɗan takarar gwamnan APGA muhimmin muƙami

"Ina godiya ga shugaban bankin Akinwumi Adesina bisa jagorancinsa da goyon wadda hakan ya taimaka min da tawaga ta wurin bayar da gundunmawar sauya bankin.

"Ina godiya bisa damar da na samu na bayar da gudunmuwa ta a bankin wurin kawo cigaba a tattalin arziki da rayuwar mutanen nahiyar Afirka."

A bangarensa, Dr Akinwumi Adesina ya nuna farin cikinsa na aiki da Blanke na tsawon shekaru uku da suka gabata.

Ya kuma yi mata fatan alheri a duk abinda ta sa a gaba.

Blanke ta fara aiki da bankin ne a farkon shekarar 2017 kuma ta jagorancin aiwatar da ayyuka da tsare tsare daban daban a cewar sanarwar.

A wani rahoton, kun ji cewa kwamishinoni uku sun kamu da cutar coronavirus (COVID-19) a jihar Gombe kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kwamishinan labarai da al'adu na jihar, Ibrahim Alhassan ne ya sanar da manema labarai a ranar Talata.

Ya ce an gano kwamishinonin sun harbu da kwayar cutar ne bayan an yi wa kwamishinoni 21 na jihar da hadiman gwamna gwaji.

Alhassan ya kuma tabbatar da cewa daya daga cikin hadiman gwamnan da 'yan majalisar jihar Gombe 5 sun kamu da kwayar cutar ta korona.

Ya ce, "A cikin kwamishinoni 21, mun samu uku da suka kamu da cutar. A cikin mashawartan gwamna na musamman, mun samu mutum daya.

"A cikin 'yan majalisun jiha, mun samu mutum biyar. Wannan shine bayanin sakamakon gwajin da aka yi wa jami'an gwamnati."

Kwamishinan ya koka da cewa annobar ta riga ta shiga cikin al'umma kuma an fara ganin yaduwar ta a cikin mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel