Kawo yanzu gawawwaki 81 muka gano - Zulum yayinda ya ziyarci Gubio (Hotuna)

Kawo yanzu gawawwaki 81 muka gano - Zulum yayinda ya ziyarci Gubio (Hotuna)

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Laraba ya tabbatar da kisan mutane 81 da jana'izarsu sakamakon garin da yan ta'addan Boko Haram suka kai Arewacin jihar ranar Talata.

Zulum ya bayyana hakan ne rabar Laraba yayinda yake hira da manema labarai a garin Felo, karamar hukumar Gubio inda harin ya faru.

Bayan kisan mutane 69 a farko, yan ta'addan sun sake komawa suka bankawa gidajen wuta.

Jimanin gwamnan ya bayyana a muryarsa yayinda yake jawabin kan irin kisan gillar da ake yiwa al'ummarsa.

Ya kara tabbatar da rahoton cewa yan ta'addan sun yi awon gaba da mutane shida.

Yace: "Har yanzu bamu kammala kirga wadanda aka kashe ba amma kun saurari maganarsu cewa a wannan makabartar an birne mutane 49, yayinda wasu iyalan sun tafi da gawawwakin yan uwansu 32."

"Kawo yanzu mun gano gawawwaki 81. Mun zo yiwa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta'azziya ne bisa kisan jiya (Talata)."

Gwamnan ya yi kira ga Sojoji su kawar da yan ta'addan daga yankin tafkin Chadi.

An yi jana'izar mutane 81 da yan Boko Haram suka kashe ranar Talata
Zulum
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Makarantarmu Obaseki ya yi karatun digirinsa - Jami’ar Ibadan UI

Harin da aka kai ranar Talata

'Yan ta'adan kungiyar Boko Haram sun kashe mutum 69 a kauyen Foduma Kolomaiye mai nisan kilomita 11 daga garin Gazaure da ke karamar hukumar Gubio na jihar Borno a ranar Talata.

Kwakwararan majiyoyi da mazauna garin sun shaidawa Daily Trust cewa yan ta'addan sun kwashe kimanin awanni biyu yayin harin kafin suka tafi.

Bayan mutanen da suka kashe, rahotanni sun ce maharan sun kashe kimanin shanu 300 kuma suka sace guda 1,000.

An gano cewa yan ta'addan sun kai hari a garin ne awanni 24 bayan sun kaiwa matafiya hari a babban titin Monguno.

Dukkan kokarin da aka yi na ji ta bakin mai magana da yawun rundunar sojoji, Col Sagir Musa ya ci tura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel