Yadda gobara ta halaka mata da 'ya'yanta uku

Yadda gobara ta halaka mata da 'ya'yanta uku

Wata mata tare da 'ya'yanta uku sun kurmushe har lahira a wata muguwar gobara da suka yi a Nkangbe, wani yanki na jihar Neja.

Gobarar ta fara wurin karfe 11 da rabi na dare inda ta dinga lashe dukiya da rayuka hudu har na tsawon sa'o'i uku.

Amma kuma, kishiyar matar mai suna Fati da 'ya'yan biyu an ceto su da miyagun kuna.

A halin yanzu suna asibiti don samun kula da taimakon likitoci, jaridar The Nation ta ruwaito.

Mijinsu mai suna Baba Abba baya gidan a lokacin da lamarin ya faru. Yana aiki a Abuja ne amma yana dawowa duk ranakun karshen mako.

Jami'an hukumar kashe gobara sun gaggauta isa bayan samun kiran gaggawa da suka yi, amma ba su samu damar cetosu ba saboda kofofi da tagogin da suka rufe.

Makwabtan sun ce basu san silar wutar ba saboda sun kwashe watanni biyu babu wuta sakamakon lalacewar tiransifomarsu.

Yadda gobara ta halaka mata da 'ya'yanta uku
Yadda gobara ta halaka mata da 'ya'yanta uku. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Karin mutum 663 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 13,464

Har a halin yanzu ba a san dalilin tashin wutar ba amma hukumar kula da gobarar na kokarin gano hakan.

Daya daga cikin makwabtansu, wanda ya shiga sahun masu bada taimako mai suna Musa Ibrahim, ya ce sun kira hukumar kashe gobara ne yayin da suka ga wutar tana tashi.

Ya ce sun yi iyakar kokarinsu wajen ceto matan da 'ya'yansu amma ba su samu damar yin haka ba saboda wutar ta gawurta.

"Mun yi matukar kokarinmu amma mun kasa shiga. Da taimakon masu kashe gobara ne muka samu fitar da amaryar tare da 'ya'yanta duk da sun kone.

"A lokacin da muka samu shiga ciki, uwargidan ta kone tare da 'ya'yanta," yace

Daya daga cikin ma'aikatan hukumar kashe gobarar ya bayyana cewa: "Mutum hudu suka rasa rayukansu amma har yanzu ba a san abinda ya kawo gobarar ba. Jama'a sun ce tiransifoma ta lalace kuma ba inji suka saka ba.

"Komai a gidan ya kone kurmus, babu abinda aka samu. Wannan abun alhini ne. Muna jiran zuwan shugabanmu don duba abinda ya faru."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel