Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya sake shan kaye a kotu
Kotun zabe ta tabbatar da Sanata Smart Adeyemi matsayin sahihin wanda ya lashe zaben kujerar wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattawa.
Kotun ta yi watsi da karar Sanata Dino Melaye saboda ya gaza gabatar da isassun hujjoji kan zargin magudin da yayi.
Dukkan Alkalan shari’ar uku sun yi ittifaki kan hakan.

Asali: UGC
Sanata Dino Melaye ya lashi takobin garzayawa kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita yan minutuna bayan hukuncin kotun inda ya ce ba zai saduda ba.
"Gaskiya ba haka muke zato ba amma mun san da ikon Allah, zamu samu adalci a kotun daukaka kara."
"Ina kira ga masoya na kada su karaya saboda wannan yaki ne kuma babu gudu, babu ja da baya."
Za ku tuna cewa Smart Adeyemi na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lallasa da kuri'u 88,373 yayinda Dino ya samu kuri'u 62,133.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng