Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa

Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa

A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar gwamnatinsa ta Aso Villa da ke babban birnin Tarayya Abuja.

Wannan shi zaman majalisar na hudu da shugaban kasar yake jagoranta ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

An fara irin wannan zama wanda ya zama doka ta farko da aka fara bi tun a zaman majalisar na makonnin da suka gabata.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, 'yan majalisar kalilan ne suka hallara a zauren da ake gudanar da taron, yayin da dama suke halartarsa ta hanyar bidiyo da aka hada da yanar gizo.

Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: UGC

KARANTA KUMA: Kwaskwarimar da aka yi wa kasafin kuɗin bana ba ta samu shiga ba a majalisar dattawa saboda kuskuren ɗab'i

An zabi sauya salon zaman majalisar ne ta hanyar ba da tazara domin kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta da manufar dakile yaduwar cutar korona da ta zamto ruwan dare.

Tun da misalin karfe 10.00 na safiyar Laraba aka fara zaman majalisar a babban dakin taro da ke fadar shugaban kasar wato Council Chambers.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari sun halarci zaman.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Babagana Monguno, shi ma ya halarci zaman majalisar.

Ministocin da a dole su na da ta cewa kuma su na dauke da bayanan da za su gabatar su ne kadai suka halarci zaman majalisar a zahiri.

An tattaro cewa, ministoci goma sun halarci zaman ta hanyar bidiyo a fafutikar da ake ci gaba da yi ta kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

Ministocin da suka halarci zaman a zahiri sun hadar da na Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, Ministan Lantarki, Saleh Mamman, Ministan Labarai da Al'adu, Lai Muhammad.

Sauran sun hadar da Ministar Kudi Kasafi da Tsare-Tsare; Zainab Ahmed, Ministan Harkokin cikin Gida; Ogbeni Rauf Aregbesola, Karamin Ministan Neja Delta; Sanata Omotayo Alasoadura.

Sai kuma Ministan Ruwa; Injiniya Suleiman Adamu, Ministar Harkokin Mata; Dame Pauline Tallen, da kuma Ministan Neja Delta; Sanata Godswill Akpabio.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel