Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan Bauchi ya warke daga korona

Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan Bauchi ya warke daga korona

Baba Tela, mataimakin gwamnan jihar Bauchi da aka yi wa gwaji aka gano ya kamu da kwayar cutar COVID-19 kimanin mako guda da ta wuce ya warke.

Rilwanu Mohammed, shugaban hukumar lafiya bai daya na jihar (BASPHCDA) ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan Bauchi ya warke daga korona
Yanzu-yanzu: Mataimakin gwamnan Bauchi ya warke daga korona. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

Idan ba a manta ba, a baya mun ruwaito cewa mataimakin gwamnan wadda shine shugaban kwamitin yaki da korona na jihar ya kamu da cutar a ranar 2 ga watan Yuni.

DUBA WANNAN: Matawalle ya bawa tsohon ɗan takarar gwamnan APGA muhimmin muƙami

Mohammed ya ce, "Kwanaki tara da suka shude, an killace mai girma mataimakin gwamnan Bauchi domin ya kamu da korona.

"Amma, mun gode ma Allah bayan da aka sake masa gwaji, sakamako ya nuna ya warke kuma yanzu an sallame shi."

Ya kuma sanar da mutwar Bello Katagum, daga daga cikin maaikatan lafiya a jihar

Ya ce, "Dr Bello Katagun, likita da ke kulawa da masu mugunyar cutar COVID-19 a jihar ya rasa ransa a bakin aiki sakamakon kamuwa da cutar."

A sakon taaziyar da ya aike, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana Katagun a matsayin jarumi a fanin lafiya a jihar kamar yadda NAN ta ruwaito.

Gwamnan ya ce, "Daya daga cikin likitocin mu ya rasu sakamakon korona. Mutum ne da ake girmamawa musamman a bangaren lafiya a Bauchi da Najeriya.

"Yana daya daga cikin kwararrun likitoci na arewacin Najeriya kuma munyi bakin cikin rashin sa.

"Yana daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar daga mataimaki na.

"Ya bamu gudunmawa sosai a Bauchi. Ya kafa asibiti, ya kula da lafiyan iyayen mu. Mutuwarsa babban rashi ne a wurin mu."

Kawo yanzu mutum 364 suka kamu da cutar a Bauchi, 224 sun warke an sallame su yayin da mutum 10 sun riga mu gidan gaskiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel