Allah ya yi wa kwamishina rasuwa a Delta

Allah ya yi wa kwamishina rasuwa a Delta

- Daya daga cikin kwamishinoni daga jihar Delta ya rasu

- Joyce Overah, kwamishina a kwamitin DESOPADEC ya rasu ne a ranar Talata da rana

- A cewar rahotanni, kwamishinan ya taba yanke jiki ya fadi ana daf da rantsar da su a 2019

Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da gwamnatinsa sun shiga alhini sakamakon rasuwar daya daga cikin kwamishinonin jihar Honarabul Joyce Overah.

Kafin rasuwarsa Overah kwamishina ne a Hukumar Cigaban Jihohin da ke Samar da Man Fetur na jihar Delta (DESOPADEC).

Kwamishinan ya rasu ne a ranar Talata 9 ga watan Yuni da rana a garin Sapele kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Yana wakiltan kananan hukumomin Sapele, Okpe da Ethiope ta Yamma ne a hukumar ta DESOPADEC.

Allah ya yi wa kwamishina rasuwa a Delta
Allah ya yi wa kwamishina rasuwa a Delta
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

An gano cewa Overah ya taba yanke jiki ya fadi a shekarar 2019 daf da rantsar da shi a matsayin mamba na DESOPADEC da Gwamna Okowa ya yi.

An kuma garzaya da shi asibiti daga wurin taron rantsarwar domin ya samu kulawan likitoci.

Kwamishinan da ya rasu yana da shekaru 50 da yan kai ya mutu ya bar yaya shida da mahaifinsa.

A wani labarin, kun ji cewa kwamishinoni uku sun kamu da cutar coronavirus (COVID-19) a jihar Gombe kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kwamishinan labarai da al'adu na jihar, Ibrahim Alhassan ne ya sanar da manema labarai a ranar Talata.

Ya ce an gano kwamishinonin sun harbu da kwayar cutar ne bayan an yi wa kwamishinoni 21 na jihar da hadiman gwamna gwaji.

Alhassan ya kuma tabbatar da cewa daya daga cikin hadiman gwamnan da 'yan majalisar jihar Gombe 5 sun kamu da kwayar cutar ta korona.

Ya ce, "A cikin kwamishinoni 21, mun samu uku da suka kamu da cutar. A cikin mashawartan gwamna na musamman, mun samu mutum daya.

"A cikin 'yan majalisun jiha, mun samu mutum biyar. Wannan shine bayanin sakamakon gwajin da aka yi wa jami'an gwamnati."

Kwamishinan ya koka da cewa annobar ta riga ta shiga cikin al'umma kuma an fara ganin yaduwar ta a cikin mutane.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta tabbatar dukkan jami'an ta sunyi gwajin ne domin ya zama abin koyi ga sauran mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel